Hadaddiyar Ƙungiyar yaƙin neman zaɓen dan takarar shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu wato YOUTH Alliance for Tinubu na ci gaba da Haɗa kan tawagar Matasa a jihar Bauchi, cikin wani taron da suka gudanar da tawagar Matasa a Jihar na Bauchi.

Taron wanda Shugaban tafiyar ƙungiyar na Jihar Bauchi Umar Lauya ya samu halarta tare da jin dukkan bukatun kowani ɓangare kana kuma ya sama ma kowani bangaren mafita tare da bada shawarwari masu ma’ana.

Cikin jawabin Nasa Umar Lauya ya bayyana cewa, tafiyar ta Tinubu ce a Jihar Bauchi kuma ta dan Takara Marshall ce, saboda haka ne yayi kira ga dukkan wadanda suka halarci taron da su zama jakadu a jihar Bauchi hsr zuwa ga nasara.

Ƙungiyar Youth Alliance For Tinubu wacce ta sauki tsawon lokaci tana hada kan Matasa a fadin Najeriya tare da nema musu mafitar da zai amfani rayuwar su tsawon lokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *