Daga Bello Hamza

Shugaban Kwamitin Tsare-Tsare na Cibiyar Tallafa wa Gajiyayyu ta A Grateful Band (AGB), Injiniya Ibrahim Abdullahi Warure, ya fallasa wani boyayyen shiri da Alkalin da ke shari’ar Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara yake da shi, bisa umarnin da aka ba shi, ba bisa shaidun da suka bayyana a gare shi ba.

Injiniya Warure, wanda ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai ranar Alhamis a Zariya, ya tabbatar da cewa Mai Shari’a Ibrahim Sarkin Yola tun farko ma bai da hurumin sauraron wannan shari’ar, balle ya yanke hukunci a kanta.

“An jiwo Alkali Ibrahim Sarki Yola yana bayyana cewa a watan gobe, ko an yarda, ko ba a yarda ba, zai yanke wa Malam Abduljabbar hukunci. Abin da muka zura ido mu gani da wacce doka zai yi masa hukunci? Wadanda suka shigar da kara sun nemi janye tuhuma a kan zagin Manzon Allah (SWA), sun ce dokar Jihar Kano ya taka. A zaman da aka kwashe shekara guda ana yi a kotun nan, ba inda aka tattauna wata kalma kan ya taka dokar kasa,” in ji shi.

Ya ce; “Ita wannan maganar da farko an fara ta ne da sunan addini, amma tun farko har }arshenta a kan karya take. Su da kansu sun karyata kansu. Wadanda suka shigar da karar ba a yi zama uku ba suka nemi kotu su janye tuhumar daga zagin Annabi (SWA), zuwa karya dokar kasa. Duniya ta san wannan. Sannan aka ci gaba da wannan karyar, har aka kai matsayin da babban Lauyan da ke jagorantarsu, Lawan Yusufari, ya fito ya yi hira da ’yan jarida, ya ce su fa duk Hadisai da Ayoyi da maganganun malamai da Malam Abduljabbar ya dauki makwanni yana kare kansa da su, babu ruwansu, saboda ba abin da suke cajinsa ba ke nan, dokar Jihar Kano ya taka.”

Injiniya Warure ya ce tun daga gwamnatin Jihar Kano, har zuwa Alkalin da ke shari’ar, sun san abin da suke tuhumar Shaikh Abduljabbar da aikatawa, kage ne kawai, ba gaskiya a ciki.

“Mutumin da ya yarda ya fito ya ce an zagi Annabi (SWA) saboda rashin jituwarsa da wani, ya san karya yake yi, ya yarda ya rabu da Allah, ya rabu da Annabi, ya rabu da lahira, ya yarda duk abin da Allah zai masa ya yi masa in dai a duniya zai samu biyan bukatarsa a kan abokin gabarsa, wannan ya kai kololuwa a gidadanci,” in ji shi.

Ya bayyana matukar damuwarsa a kan yadda ’yan siyasa da Malaman Maja ke amfani da sunan Annabi (SWA) da nufin cimma burinsu a kan Shaikh Abduljabbar. “Sun san abin da suke fada ba gaskiya ba ne, amma suka ci gaba da yi don cimma bukatar duniya,” in ji shi.

Ya kara da cewa; “Kun san a sati na uku da faruwar lamarin nan, gwamnati ta fitar da kudade har Naira miliyan 300, wai za ta raba wa ’yan fim din Kannywood a yi fina-finai don a tabbatar Malam Abduljabbar ya zagi Manzon Allah (SWA)? Akwai zaman da muka yi da muka yi shagube a kan maganar, shi ya sa gwamnati ta janye. Me ya kawo ’yan Kannywood cikin maganar zagin Manzon Allah (SWA)? Me ya sa ake son tunzura jama’a.”

Injiniya Abdullahi Warure, wanda ya tabbatar da cewa duk abin da yake fada a kan gwamnati ko Alkali Ibrahim Sarki Yola, ba jita-jita ba ce yana da hujjoji, sai ya samu tabbaci yake magana a kai, ya ce; “Gwamnati da Malaman Maja da Alkali sun dauka abin da ya faru shekara 200 zai iya faruwa yanzu, sai dai suka shiga ne suka fahimci abin ba zai yiwu ba.”

Da yake tsokaci a kan shige-da-facen da wasu ke yi don ganin an yanke wa Shaikh Abduljabbar ko da kuwa ba a same shi da laifi ba, Injiniya Warure ya nuna matukar mamakinsa a kan yadda Shaikh Karibullahi Nasiru Kabara ya tare a Abuja yana kamun a kafa don neman ganin an yi watsi da daukaka karar a kan bukatar a yi adalci a shari’ar da Barista Dalhatu Shehu ya shigar a wata babbar kotu.

Daga karshe Injiniya Ibrahim Abdullahi Warure, ya jaddada cewa suna bin wannan maganar yadda ta dace, kuma za su dauki matakan da suka yi daidai da doka da shari’a a kan duk wanda yake da hannu wajen musgunawa ko take hakkin Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara.

 

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *