Daga Ibrahim Muhammad Kano

Cibiyar kula da al’adu da wayar dakai ta Najeriya”National Institute for Cultural Orientation. NICO “ta  gudanarda taro bita  na wayar dakai musamnan ga yan jarida sakamakon rawarda suke takawa wajen takarawa wajen samarda zaman lafiya.

Babban sakataren cibiyar Alhaji   Ado Muhammad Yahuza ya bayyana cewa kasancewar kasarnan ta hada jinsi daban-daban kuma abubuwa suna faruwa faruwa na rashin tsaro a bangarori da dama da yakamata duk abinda zasu rubuta ya zama wanda zai kawo hadin-kai ne a kasarnan ya kawo dankon zumunci a tsakanin al’umomi na kasarnan.

Ya ce in babu zaman lafiya a kasa ba abinda za’a iya domin akwai kasashe a Dunuya da yau zaman lafiya ya gagaresu sun gudu sun bar kasar duk abinda ka tara in rigima tazo za’a gudu a bari wannan na daga dalinda yasa Duke gudanarda taron bitar.

Ado Muhammad Yahuza ya bayyana yada labaran karya ko baza jita-jita da ake wannan na faruwane saboda  wasu  basuda kwarewa  a  aikin jarida da kuma musamnan a kafofin sada zumunta kowa ya shigo mutane da waya a hannunsu wani na kwance a dakinsa yayi karya ya fada ba tareda tunanin abinda zai je ya dawo ba.

Yace yakamata Gwamnati ta shigo da dokoki da za’a rika hukunta mutane masu karya da yada jita-jita sannan kuma a rika wayar da kan mutane,domin wasu bada gangan suke ba,ba su ma san me suke ba da yanda abin zai je ya dawo ba.

Yahuza Ado ya ce a taron bitar akwai kasidu da suke magana akan wayar da kan mutane akan abubuwa da ake marasa amfani a kafofin sada zumunta ana sa hotunan karya ana yadawa wanda da hakan bai dace ba.

Shima da yake zantawa da yan jarida shugaban kungiyar yan jariudu na qasa reshen jihar Kano.Kwamared Abbas Ibrahim yace taron da aka shirya dan zaburarda yan jarida kan gudummuwarda za su bayar dan tabbatarda zaman lafiya da bada rahoto akan kalubalen tsaro abune daya dace da kuma ya zo a kan gaba.

Ya ce shi sanarda al’ummar abubuwanda suka dace na taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya,wannan abune na tarbiyya da ladubban aikin jarida wannan bita abune kawai na sake zaburantarwa domin mahalarta bitar mutum 50/yan jarida mahalarta bitar su sake kaimi su gujewa abuwanda ba dace ba,suyi abinda yakamata dan samarda zaman lafiya da kwanciyar hankali sabanin ingiza wuta da tada tarzoma.

Abbas Ibrahim yace duk wanda baya aiki bisa ka’idoji na aikin jarida ba dan jarida bane, saboda dama wadannan su suke nuna aikin jarida ko sabanin haka kuma a kowane aiki akwai nagari da bata gari wanda baya aiki da kamar yanda yakamata bata bari ne,kuma kungiyar yan jarida na da matakai na ladabtarwa idan aka kama mutum.

 

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *