Dan takarar gwamna a karkashin inuwar Jam’iyyar PDP a Kaduna, Isa Ashiru Kudan ya bayyana cewa al’ummar jihar na cikin kunci a karkashin mulkin Gwamna Nasiru El-Rufai.
Inda Isa Ashiru Kudan ya yi kira ga gwamnan da ya janye korar ma’aikata da yake yi ba ji ba gani; “ina kira ga Mallam Nasiru Ahmad El-Rufai da ya dakatar da koran ma’aikata da yake ci gaba da yi, al’umma jihar Kaduna a halin yanzu suna fuskantar matsaloli rayuwa daban-daban, idan ba a tallafa musu ba to bai kamata a ce ana raba su da ayyukan da suka dogara da shi don ciyar da iyalansu ba, korar ma’aikata a wannan yanayi na tsadar rayuwa shi ne mafi munin nau’in zalunci”, inji shi.
Idan za a iya tunawa Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da korar malamai 2,356, da suka gaza cin jarrabawar gwaji da aka yi musu ciki harda shugaban Kungiyar Malamai ta Nijeriya reshen jihar.