Rahotanni Sun bayyana cewa Lukaku na Shirin komawa Inter a matsayin bashi Kasa da shekara daya bayan da ya Sanya hannu kan Kwantaragin fam Miliyan Casa’in da bakwai da rabi £97.5 in da ya koma Stamford Bridge a watan Augustan shekarar da ta gabata.

A yanzu haka Thomas Tuchel ya amince da komawar Lukaku ga tsohon Kocin sa San Siro, bayan da Chelsea ta amince ta karbi fam Miliyan takwas da rabi (£8.5m) a matsayin kudin da ta kashe wajen siyan sa daga Inter.

Da alamu Chelsea na duba Yiwuwar karbar Lautaro Martinez, Denzel Dumfries, Milan Skriniar and Alessandro Bastoni domin barin Lukaku ya Koma Inter.

By Editor

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *