Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce abin da ya sa bai cire tallafin man fetur ba shi ne don gudun tsananta wa al’ummar ƙasar.
Shugaban ya fadi hakan ne a wata hira ta musamman da ya yi da jaridar Bloomberg ta intanet ta Amurka da aka wallafa a ranar Talata.
Bloomberg ta tambayi Buhari cewa me ya sa ya ƙi amsa kiraye-kirayen da Asusun ba da lamuni na duniya IMF, da Babban Bankin Duniya ke masa tsawon shekaru na ya janye tallafin fetur kuma canjin kuɗaɗen ƙasashen waje su zama na bai ɗaya?
Sai ya amsa da cewa har yanzu akwai ƙasashen yammacin duniya da ke bin tsarin biyan tallafin fetur.
“To me ya sa za mu janye namu a yanzu?
“Abin da ƙasashen waje ke fama da shi shi ne sun fi mayar da hankali kan tsare-tsaren da aka yi a rubuce amma suna mantawa da tasirin haka ga al’ummominsu,” in ji shi.
A bara ne gwamnatin Shugaba Buhari ta so janye tallafin mai, “amma bayan tuntuɓar masu ruwa da tsaki da yadda abubuwa suka kasance a bana, ɗaukar matakin ba mai yiwuwa ba ne.
Sai dai ya ce ƙara samar da albarkatun fetur a cikin ƙasar ta hanyar sababbin matatun mai da ake sa ran za su fara aiki nan gaba a wannan shekarar za su taimaka sosai.
Kan batun tsadar kuɗaɗen ƙasashen waje da mayar da farashinsu na bai ɗaya kuma shugaban Najeriyar ya ce hakan na faruwa ne sakamakon wasu abubuwa da ke faruwa a wajen kasar.
“Idan aka ci gaba da samar da mai a cikin gida da tsare-tsaren samar da abinci, za a samu a daidaita farashin kuɗaɗen da mayar da su bai ɗaya a gwamnatance da kasuwar bayan fage.
Sauran tambayoyin da aka yi wa Shugaba Buhari
Ba tambayar tallafin man fetur kawai Jaridar Bloomberg ta yi wa shugaban na Najeriya ba, ta yi masa tambayoyi kan tsaro da yaƙi da cin hanci da kuma tattalin arziki.
An tambaye shi kan ko yaya yake ganin ƙoƙarinsa kan alkawuran da ya dauka a hawansa mulki musamman na yaƙi da cin hanci da farfaɗo da tattalin arziki.
Sannan an tambaye shi kan ko me ya sa ya kasa shawo kan matsalar tsaro a ƙasar har yanzu?
Shugaba Buhari dai ya amsa cewa Najeriya ta samu ci gaba sosai fiye da yadda ya same ta.
Ya ce a yanzu ba a cin hanci ƙarara kamar da, kuma ƴan Najeriya na jin ƙwarin gwiwar fallasa masu satar kuɗin gwamnati ba tare da tsoro ba, kuma ana mayar da kuɗaɗen ga hukumomi.
Sai dai ko a makon da ya gabata sai da hukumar da ke yaki da rashawa ta EFCC a Najeriyar ta ce ‘yan ƙasar sun sare da kwarmata bayanai kan masu satar kudin gwamnati, duk da ɗumbin kudin lada da ke tattare da yin hakan.
Shugaban hukumar ta EFCC, Abdullahi Bawa ne ya faɗi hakan ne a lokacin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a jihar Kwara.

Tsaro da tattalin arziki
Kan batun matsalar tsaro, Buhari ya shaida wa jaridar Bloomberg cewa a yanzu babu wani yanki da ke ƙarƙashin ikon yan ta’adda a ƙasar, kuma shugabannin masu ta da ƙayar bayan sun mutu.
“A shekarar 2015 Boko Haram na iko da fadin yankin da ya kai girman ƙasar Belgium a kan iyakokin Najeriya
“A watan Maris harin sojin saman Najeriya ya hallaka shugaban ƙungiyar ISWAP.
“Gwamnatocin baya ba su samar da jiragen yaƙin da Amurka ta shawarta a nema ba, mu mun samar kuma hakan ya zama wata kafa ta sabunta ƙawancen Najeriya da ƙawayenmu na yamma.
Sai dai shugaban ya zargi ƙasashen yamman da ƙin ba da hadin kai wajen magance barazanar ƙungiyar IPOB.
Ya ce: “Mun ayyana IPOB a matsayin ƙungiyar ta’addanci amma ƙasashen yamma sun bar shugabanninta suna cin karensu babu babbaka suna yaɗa kalaman ƙiyayya daga Ingila. Dole a kawo ƙarshen hakan,” in ji shi.
Ya kuma yi tsokaci kan rikicin manoma da makiyaya da ya ce gwamnatinsa ce ta kawo ƙarshen lamarin da aka shafe gomman shekaru ana fama da shi.
Hauhawar farashi
An tambayi Shugaba Buhari kan ko me ya sa hauhawar farashi ya ƙaru da ɗigo biyu tun 2015, duk da ƙoƙarin da yake cewa gwamnatinsa na yi don haɓaka ɓangaren noma?
“Da ba mu samar da tsare-tsaren haɓaka samar da abinci a cikin gida ba da ban san a wane yanayi hauhawar farashi za ta kasance ba a yau.
“Kuma har yanzu ba mu ga samar da isasshen abincin da ake buƙata ba a cikin ƙasar,” amsar da ya bayar kenan.
Ya c gaba da ccewa tsare-tsare kamar shirin tallafa wa manoma don rage shigo da kayan abinci marar inganci ya haɓaka noman shinkafa daga ton miliyan 5.4 da ake samarwa a 2015 zuwa ton miliyan tara a 2021.
Wajen amsa tambayar ƙoƙarin da ya yi a tattalin arziki, Shugaba Buhari ya ce ya shafe shekarun mulkinsa wajen zuba jari sosai a gina titunan mota da na jirgin ƙasa da gine-ginen harkokin sufuri don samar da ci gaba da haɗa al’ummomi a sauƙaƙe.
“Ba lallai a ga sakamakon a yanzu ba, amma lokaci zai nuna hakan,” a cewarsa.