Jami’an Morocco sun ce adadin wadanda suka mutu sakamakon yunkurin da ‘yan ci-rani ‘yan Afirka suka yi daga arewacin kasar na shiga yankin Melilla na Spain da karfin tsiya ya kai mutane 23.

Da farko dai jami’ai sun ce mutane biyar suka mutu, a lokacin da bakin-haure kusan 2,000 galibinsu ‘yan Afirka daga kudu da Sahara suka tunkari kan iyakar kasar Morocco da Spain, da safiyar Juma’a.

Wani jami’in kasar Morocco daga garin Nador da ke kusa da kan iyaka ya ce jami’an tsaro 140 da bakin-haure 76 suka jikkata yayin arrangamar da suka yi, a lokacin da suke yunkurin tsallaka kan iyakar, zuwa cikin Spain.

Yayin da yake bayyana bacin ransa kan aukuwar lamarin, Fira Ministan Spain ya bayyana tururuwar da bakin bakin-hauren suka yi cikin yankin Melilla daga Morocco a matsayin hari da aka kai wa ‘yankin kasar Spain, yayin da masu rajin kare hakkin bil’adama suka bukaci a gudanar da bincike.

Fiye da mutane 500 ne suka yi nasarar shiga yankin dake kula da kan iyaka bayan yanke katangar wayar da suka yi.

By Editor

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *