A ranar Juma’a ne kungiyar Lauyoyi Mata ta Duniya, (FIDA), reshe yankin babbar birnin tarayya Abuja, ta bukaci masu kada kuri’a dasu nisanci dukkan nau’in tashin hankali su kuma gujewa shiga harkokin bangar siyasa yayin harkokin zaben 2023 da ke tafe.

Wata babbar jami’a a kungiyar, Esther Ikenye, ta bayyana haka a taron fadakar da al’umma da kungiyar ta gudanar a kauyukan Kori da Kofai da ke karamar hukumar Bwari, shirin ya samu tallafin ‘Action Aid.

Ta nemi ‘yan Nijeriya da su yi amfani da karin wa’adin da aka yi na yin rajista don tabbatar da sun mallaki katin su na kada kuri’a.

“Baban dalilin gangamin shi ne don fadakar da al’umma a kan rajistan katin zabe wanda yana daga cikin muhimman tanade tanaden dokokin zabe na wannan shekarar.

“Haka kuma don tabbatar da shigar mata da masata cikin harkokin zabe da tafiyar da gwamnati musamman ganin zaben 2023 na nan tafe,” in ji ta.

A jawabinsa, Sakataren Hakimin Dutse Alhaji, Mista Hamzat Zakaria, ya ce, lallai sun amfana da gangamin sun kuma karu kwarai da gaske, ‘An bamu shawarar karbar katin zabe a matsayin babbar hanyar sauke nauyin da ke kan mu na zaban wadanda za su jagorance mu a shekaru masu zuwa.

Ya kuma yi alkawarin kiran taro don sanar da wadanda basu samu halatar wannan taron ba don suma su amfana.

ReplyForward

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *