Daga Bello Hamza

Ɗan takarar gwamnan Jihar Zamfara, Dr. Dauda Lawal ya yi zagayen ta’aziyya da jajantawa ga mutanen da aka yi wa rasuwa da waɗanda ibtila’i ya faɗa wa.

A jiya Lahadi bayan ya kammala amsan gaisuwar sallah, ɗan takarar gwamnan a ƙarƙashin tutar jam’iyyar PDP ya zagaya don yin ziyarar ta’aziyya fadin Jihar Zamfara.

A lokacin ziyarar, Dauda Lawal ya ziyarci iyalan marigayi Alhaji Ibrahim Nabature, wanda

Cikin jerin ziyarorin ta’aziyyar da dan takarar na PDP ya kai, akwai gidan marigayi Malam Bashir Nurul Aulad wanda Allah Ya yi wa rasuwa a makonnin baya. Daga nan ya zarce gidan marigayi Alhaji Sa’adu Maishadda wanda shi ma ya rasu a kwanakin baya.

Haka nan kuma Dauda Lawal ya ziyarci kasuwar Bebeji Plaza inda ya jajantawa shugabancin kasuwar bisa ibtila’in garkuwa da aka yi da wasu ‘yan kasuwar har mutum 20. Idan dai ba a manta ba, a kwanakin baya ne ‘yan bindiga suka sace ‘yan kasuwar a hanyarsu daga Jihar Sakkwato zuwa Gusau. Wanda daga baya Allah Ya kubutar da ‘yan kasuwar.

Duk cikin ziyarar jajantawar, Dauda Lawal ya ziyarci gidan Honorabul Abubakar Bello Furfuri domin yi masa jaje bisa garkuwa da ‘yan bindiga suka yi da ‘ya’yansa guda shida. Gamjin na Gusau, Dauda Lawal ya yi addu’ar Allah Ya kubutar da su, Ya basu mafita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *