Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnati, Abubakar Malami, ya ba da tabbacin cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai dawo da Najeriya kan tafarkin zaman lafiya kafin ya bar mulki a 2023.

Ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Birnin Kebbi, domin taya Musulmi murnar Sallar Layya.

Malami ya ce sam Buhari ba ya barci, ba wai kawai don ganin ya mika mulki cikin ruwan sanyi ba, yana ma kokarin ganin ya kawo karshen matsalar tsaron da ke addabar kasar.

Ya ce, “Ina so in tabbatar muku da cewa gwamnatin Buhari za ta ci gaba da yin dukkan abin da ya kamata wajen dawo da tsaro a Najeriya.

“Muna addu’ar Allah ya amsa addu’o’inmu, ya dawo da zaman lafiya a Jihar Kebbi da ma kasa baki daya, da kuma tabbatar da mika mulki cikin ruwan sanyi a badi,” inji Malami.

A ranar 29 ga watan Mayun 2023 ce dai wa’adin Buhari zai kare

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *