Daga Umar Faruk Brinin Kebbi

Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a Dr. Abubakar Malami, SAN ya bayyana cewa” gwamnatin Buhari za ta yi duk Mai yiwuwa wajen tabbatar da tsaron kasar nan, ina addu’ar Allah ya karbi addu’o’inmu don samu wawwamammen zaman Lafiya a kasarmu Nijeriya da Jihar kebbi kabi daya.

Ministan Abubakar Malami ya bayyana hakan ne a cikin sakon murnar sallar ga al’ummar Musulmin kasa da na Jihar Kebbi da ma sauran sassan Jihar kan murnar zagayowar Sallar Eid-al-adh na bana.

Minista ya ce” Eidul Adha tana tunatar da musulmi da su kasance masu biyayya da zuciya daya ga umarni da dokokin Allah Madaukakin Sarki kamar yadda Annabi Ibrahim, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takarar da Sakataren yada labaru Ibrahim Abubakar Dakingari na Kungiyar Khadimmiya da ya sanyawa hannu a kuma rabawa manema labaru a Brinin Kebbi.

“Yayin da muke gudanar da wannan gagarumin biki, ya kamata mu yi tunani a kan darussa na asali na hakuri, sadaukarwa da mika wuya ga yardar Allah da Annabi Ibrahim ya nuna a lokacin da Allah ya umarce shi da ya yanka dansa tilo (Isma’ila), ta hanyar sadaukar da kanmu ga kara riko da Dokokin Ubangiji da kuma nuna hakikanin ruhin Musulunci a cikin dukkan ayyukanmu” Malami ya yi nasiha.

“Yayin da mike bikin Eidul Adha, dole ne mu yi la’akari da duk abubuwan da ke faruwa a kasarmu, domin mu yi amfani da lokacin yin addu’a don Allah ya kawo mana dauki ga matsalolin tsaro da tattalin arziki da ke addabar kasar nan wanda gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke ciki, inji shi”.

Haka Kuma Ministan ya kuma yi kira ga ’yan’uwanmu maza da mata a kasa mai tsarki da suke gudanar da aikin hajjin bana da su yi ta addu’a domin neman fansa.

“Ina kara sake tabbatar muku cewa gwamnatin Buhari za ta ci gaba da yin duk mai yiwuwa wajen tabbatar da tsaron kasar nan, ina addu’ar Allah ya karbi addu’o’inmu na ganin an samu dawwamammen zaman lafiya a jihar Kebbi da kasa baki daya tare da samar da zaman lafiya a siyasance. mika mulki farkon shekara mai zuwa, inji Minista Malami”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *