Daga Bello Hamza
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar Benuwai, (SEMA) ta bayyana cewa, an haifi jarirai 80 a sansanin ‘yan gudun hijira na jihar a cikin wata 7.
Babban sakataren hukumar, Dakta Emmanuel Shior, ya sanar da haka a yayin raba kayan abinci a sansanin da aka saba yi duk wata. Ya ce, hukumar ce ta dauki qiddigar haihuwar da aka yi a cikin sansanin.
Ya kuma kara da cewa, masu gudun hijitrar na zaune ne da matansu hakan ya sa aka samu yawan haihuwar a sannasanin. Hukuar ta sanya dokar hana mu’amala a tsakanin mata da maza wanda ba ma’aurata ba ne.
“Yana da matukar wahala a iya dakatar da yawan haihuwar da ake a sansanin don suma ‘yan gudun hijira mutane ne.
“Cikin a’al’adar dan adam shi ne ya yi jima’i ko da kuwa bashi da abinci, kuma a duk inda ya samu kansa zai iya yin jima’in koda kuwa a sansanin gudun hijira ne.
“Bangaren da muke iya magani shi ne na hana wadanda ba ma’aurata ba su rinka saduwa da juna da kuma ayyukan badala a sansanin,” in ji shugaban hukumar ta SEMA.
Hukumar ta raba buhunan shinkafa 3,000 na masara 2,000 da sauran kayyakin masarufi.