Daga Abubakar Abba, Kaduna

Wasu mutanen ne bai wa  masu damfara a kafar yanar Gizo danar da suke yi masu damfarar kuxaxen su ta hanyar bayanan su da suke tura wa masu damfarar.

Furucin hakan ya fito ne daga bakin wani matashi sanan ne a fannin kwamfuta da kuma haxa manhajar zamani Adamu Abubakar Sadiq.

Adamu a hirarsa da Leadership Hausa a kaduna ya yi nuni da cewa, wasu masu ilimi a fannin kwamfuta ne ke yin amfani da damar da suka samu ta ilimi da qware wa a kwamfuta ke yin amfani da damar wajen damfarar mutane kuxaxen su ta hanyar yin amfani da yanar Gizo.

Matasahin wanda kuma shi ne ke jagorantar tafiyar da kamfanin harkar Yanar Gizo wato Deecompt System Kaduna ya qara da cewa, akasarin masu yin damfarar, suna tura wa mutane saqon karta kwana a wayar su ta tafi da gidan ka, inda  za su buqaci bayanan su na bankunan da suke yin ajiya daga nan sais u damfare su.

Ya ci gaba da cewa, idan mutane suka kasance ko dai ba su da cikakken ilimin boko ko kuma ma su son banza ne ko kuma waanda qaddara ta aukawa, sai  suka tura wa masu damfarar bayanan sun a ajiya a bankun,  sai damfare su.

Adamu ya sanar da cewa, idan har bas u da bayanan mutune na banki, zai yi wuya su yi masu damfara, inda ya shwarci mutane da su gane cewa, duk wanda ya buqaci bayanan su na banki, ta hanyar saqon karta kwana da aka tura masu a waya, kar su bayar.

Da yake yin tsokaci kan wasu daga cikin manyan nasarorin da kamfanin na su ya samu Adamu ya ce, “ Mun fi bayar da qarfi a vangaren haxa manja watoa turance, soft wirekamar ta haxa jarrabawar JAMB wace za ta taimaka wa xaliban da za su zana jarrabawar”.

Ya ce, “Mun kuma horas da kimanin xalibai 50 kan yadda z asu zana jarrabawar ta JAMB wani lokacin kuma, mukan je har wasu jihohi domin bayar da irin wannan horon”.

A kan shiye-shiyen da kamfanin ke yi a shekara mai zuwa, Adamu ya ce,” In sha Allah, muna son mu haxa wata manhaja ta Wi-Fi wacce ba sai mutum ya yi amfani da Data ba, wacce za ta baka damar shiga kafar yanar Gizo  kai tsaye.

Adamu ya kuma yi kira ga, musamman matasan da ke a Arewacin qasar nan da suka kammala makaratun gaba da sakandare suke kuma zaune ba su da aikin yi,  da su rugumi koyon ilimin kwmfuta don su zama masu dogaro da kansu ba tare da sun ci gaba da jiran aikin gwamnati ba.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *