Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Bisa la’akari da karuwar rashin aikin yi a tsakanin matasa da ke addabar jihar Zamfara, a yau jam’iyyar African Democratic Congress ADC reshen jihar Zamfara ta kaddamar da horar da matasa da mata 200 kan sana’o’i daban-daban.

Da yake jawabi a wajen bikin kaddamarwar, shugaban jam’iyyar na jiha Hon. Kabir Garba Gusau ya ce jigon shirin na ADC a jihar shi ne ya samar da guraben aikin ga marasa aikin yi musamman a tsakanin mata, don haka akwai bukatar su zama masu dogaro da kawunansu.

Ya ce matakin ya yi dai-dai da shirin Jam’iyar ADC na 2023, kuma idan aka zabe shi a kan karagar mulki a jihar, za ta yi duk mai yiwuwa wajen dakile matsalolin rashin tsaro da fatara da yunwa da rashin aikin yi a tsakanin mata da matasa masu tasowa.

Honorabul Kabir Garba ya bukaci wadanda suka ci gajiyar shirin da su kara maida hankali wajen samun sana’o’i maimakon dogaro da aikin Gwamnati, ya kara da cewa lokaci ya yi da mata da matasa za su tsunduma kansu cikin sana’o’i daban-daban domin su kasance masu dogaro da kai da kuma amfani ga al’umma.

A nata jawabin shugabar mata ta Jam’iyar ADC ta jihar, Hajiya Maryam Abdullahi ta ce shirin zai rage guraben aikin yi tare da samar da guraben ayyukan yi ga matan jihar, inda ta bayyana cewa sana’o’in da za a horas da su sun hada da dinki, kayan wanke-wanke, kayan ado da sabulu, da dai sauransu su.

A nasu Jan hankalin da shawarwari dan takarar Gwamnan Jihar na Jam’iyar ADC Comrade Jafaru Salisu, da mai neman kujerar Sanata mai wakiltar mazabar Zamfara ta tsakiya Nuhu Garba Tunau, da dan takarar mazabar tarayya Honorabul Aliyu Sani Tsafe da dan takarar mazabar Gusau1 Honorabul Yusuf Aliyu Galadima sun bukaci mahalarta taron da su tabbatar sun maida hankali. a kan abin da za a koya musu domin su amfana da abin da aka koya masu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *