Daga Bello Hamza

Majalisargudanarwa ta hukumar kula da iyakokin ruwa na kasa-NIMASA ta amince da nada sabbin daraktoci uku.

Sabbin daraktocin sune Mr Otonye Obom, Kyaftin Umoren Sunday Michael da kuma Mr Kazir Abubakar Musa.

An dai nada sabbin daraktocin ne tare da muqaddashin daraktoci guda goma sha takwas da kuma mataimakan daraktoci guda ashirin.

Har ila yau, hukumar ta amince da karin girma ga ma’aikata dari hudu da talatin da daya zuwa mataki na gaba.

Hukumar ta amince da wadannan karin girma ne a taron majalisar gudanarwa na hukumar wanda ya gudana a shedikwatar ta dake birnin Ikko.

A jawabin shi, Shugaban hukumar, Dr Bashir Jamoh, ya taya ma’aikatan murnan karin girma da suka samu, sannan ya hore su da su jajirce wajen cimma muradan hukumar.

Ya kuma yi kira a gare su da su dauki wannan karin girma a matsayin kwarin gwiwa don cimma manufar da aka sanya a gaba.

Dr Bashir Jamoh ya kuma tunatar da su akan muhimmancin tabbatar da cewa sun inganta jin dadi da walwalar sauran ma’aikata don karfafa masu gwiwa wajen bada himma da maida hankali wajen aiki.

Ya kuma sha alwashin cewa hukumar a karkashin jagorancin shi, zata tabbatar da cewa ana gudanar da karin girma ga ma’aikata a lokacin da ya dace da kuma horas da su don bada gagarumar gudunmawa wajen inganta tattalin arzikin kasa.

Hukumar gudanarwan a nata bangaren, ta bukaci wadanda suka samu karin girman da su kara bada himma wajen hidimtawa hukumar, tana mai tunatar da su cewa karin girma na zuwa ne da karin nauyi.

Wannan karin girma shine karo na uku a karkashin jagorancin Dr Bashir Jamoh tun bayan nada shi shugaban hukumar a watan Maris na shekarar dubu biyu da ashirin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *