A ranar Lahadi 21 ga watan Agustan 2022, Asibitin MGK Healthcare Services dake garin Kano ta tarbi kwararrun likitocinta dake kasar Misra a karkashin yarjejeniyar fahimtar juna dake tsakaninta da Cibiyar lafiya ta Medica Overseas dake Misra.

Tawagar Asibitin na MGK Healthcare Services ta tarbi tawagar liktocin ne a filin sauka da tashi na Malam Aminu Kano dake garin Kano. Inda bayan tarbar kai tsaye aka garzaya da su zuwa Asibitin dake titin Karkasara dake karamar hukumar Tarauni a cikin garin Kano.

Wanda ya assasa kuma shugaban Asibitin, Malam Muhammad Garba, ya gabatar da ma’aikatan Asibitin ga bakin likitocin, inda aka gabatar musu da mukaman kowannensu.

Da yake ganawa da manema labarai, wanda ya assasa kuma shugaban Cibiyar lafiyar, Malam Muhammad Garba, ya ce daga cikin alfanun da al’umma za ta samu daga yarjejeniyar fahimtar junar da suka yi da Medica Overseas na kasar Misra shi ne bunkasa ayyukansu wanda idan aka cimma hakan al’umma ce za ta amfana domin za a kula da lafiyarsu yadda yakamata. Inda ya ce; “wadannan baki namu daga Misra suka zo, sanannen abu ne tun zamani mai tsawo kasar Misra sun yi nisa ta harkar lafiya ba kawai a nahiyar Afrika ba, harma da duniya baki daya. Muna ganin alakar da za mu kulla tare da su, zai zama mu ma mun karu da wani ilimin da suka sani zuwan su nan”, ya nusasshe.

Ya ci gaba da cewa; “sannan kuma da yawa daga cikin mutanenmu da suke yin tafiye-tafiye neman lafiya zuwa Misra, tunda yanzu muna tare da ‘yan Misra din zai zama an takaita musu zirga-zirgar zuwa can wurin na su. Domin mutanen da za su je su tarar a can, sune muke tare da su a nan birnin Kano”, ya jaddada.

Da yake bayyana manufar zuwan bakin likitocin, Malam Muhammad Garba ya ce; “bakin da muka tarba abokan aikinmu ne, wadanda muka kulla yarjejeniyar fahimtar juna a watannin da suka gabata domin gudanar da aiki a tare wajen inganta harkar lafiya baki daya. Akan wannan ne daya daga cikinsu, ya zo ya zauna tare damu na dindindin ya zama ya taimaka ya kara inganta abubuwan da muke gabatarwa a halin yanzu na kula da marasa lafiya tare da takaitawa mutane fita kasashen waje neman lafiya”, ya nusasshe.

Ya kuma lurantar da cewa ba gasa suke yi da Cibiyoyin lafiya na gwamnati ba, illa iyaka suna tallafawa gwamnatin ne wajen bunkasa lafiyar al’umma baki daya. Domin gwamnati kadai ba za ta iya kula da baki dayan al’umma ba.

Inda ya ce; “Harkar lafiya harka ce da take da bukatar gudummawar kowa da kowa. Idan ya zama an samar da wani waje da zai agazawa kokarin da gwamnati take yi. Mu ba muna kallon kanmu a matsayin kishiyoyi bane ko masu yin tsere da gwamnati. Muna ganin cewar mutane ne da za mu bada tamu gudunmawar. Gwamnati na yin na ta kokarin, amma tana bukatar ya zama an tallafa mata daga waje. Kuma wannan shi ne abin da ke faruwa a kusan kowanne fanni na rayuwa za ka ga mutane dake fannin masu zaman kansu, za ka ga na su gudunmawar ke nan da suke bayarwa domin ganin an inganta harkar lafiya. Wajen lura tare da mutane, rage yawan cunkoson mutanen dake asibitocin gwamnati, da samun kwararru akan lokacin da ake da bukata.

Sannan ya kuma yi bayani dangane da ayyukan asibitin na MGK Healthcare, inda ya ce asibiti ne na kwararru da yake yin ayyuka daban-daban wanda ya hada da bangaren masu kula da ciwon hakori, bangaren bayar da magunguna, bangaren gwaje-gwajen cututtuka manya da kanana, bangaren da ke haska cututtukan dake jikin mutum, bangaren tiyata da ya hada da na kashi, karbar haihuwa, cututtuka, kwakwalwa da jijiya da kuma na zuciya, sannan suna da bangaren zirga-zirga da marasa lafiya da sauran su.

A yayin zaman tattaunawar a Asibitin, Malam Muhammad Garba, ya yi wa bakin maraba da zuwa tare da yi musu tilawar ayyukan Cibiyar da abin da take so ta cimma.

Da yake maida jawabi, Babban Daraktan Cibiyar lafiya ta Medica Overseas dake kasar Misra, Dr. Thamar Kazamel, ya bayyana cewa ya ji dadin yadda aka tarbe su fiye da tunaninsu. Inda ya yi alkawarin ganin sun fito da sabbin tsare-tsaren da zai bunkasa ayyukan asibitin. Tare da inganta yadda ake kula da marasa lafiya wajen ganin an samu nasara kan abin da suka sanya a gaba. “zamu samar da akwatin jefa korafi domin mutanen dake hulda damu su samu damar isa gare mu cikin sauki”, inji shi.

Dr. Kazamel ya kuma jaddada cewa za su samar da jami’i na musamman da zai rika kula da bukatun marasa lafiya da sauran al’ummar da suke hulda da su. “sannan zamu samar da dukkanin abin da ake da bukata ga marasa lafiyarmu. Za mu kuma taimakawa marasa lafiyarmu wajen ganin sun samu lafiya a ko’ina ne a fadin duniyarnan. Ba kawai za mu kula da lafiyar ku bane, za mu kula da ku fiye da yadda kuke tsammani”, ya tabbatar.

Dr Kazamel ya kuma kara da cewa daga cikin abin da za su bunkasa akwai batun kula da marasa lafiya a nan gida kamar suna kasashen waje.

A karshe ya yi fatan samun hadin kan sauran ma’aikatan asibitin domin cimma manufar da aka tsara wajen kai Asibitin gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *