Daga Idris Umar Zariya

Mai Martaba Sarkin Gombe Alh Abubakar Shehu Abubakar III. A Ranan Lahadi 31/July2022. Yatabbatar ma Alhaji Adamu Aliyu da Sarautan Gargajiya a Matsayin Sarkin Samarin Gombe na Farko a Masarautan Gombe dake Jahar Gombe.

Anhaifi Alh Adamu Aliyu ne a Shekaran 1993. Yayi karatunsa na Addinin Musulunci kaman yadda tsarin al’adan Fulani yake a Arewacin Nigeria Sannan yayi karatun Zamani
LEA PRAMARY School Bolari Gombe 2002 Zuwa 2008, Govt Secondary School Juinio Zuwa Senior 2008 to 2011. Bayan Kammala Secondary Saiyawuce Zuwa Abubakar Tatari Ali Polytechnic Bauchi Daga 2014 zuwa 2018 Computer Science,

Adamu Aliyu Yafito Daga Zuri’an gidan Sarkin kifin Gombe ‘dane Wajen Alh Aliyu Sarkin Kifi, Allah ya Azurtashi da Son Al’umman Musamman Matasa kaman Yadda yatashi yagani a gidansu wajen hidiman Al’umman
Kuma yakasance Dan kasuwa Mai kishin Matasan Jahar Gombe,

Mai Martaba Sarkin Gombe Alh Abubakar Shehu Abubakar III. Yace sunyi Sarautan Sarkin Samarin Gombe ne Saboda kyakkyawar alakanshi ga Masautan Gombe da Matasan Jahar Gombe Wajen kokarin shi na ciyar da Al’umman gaba da Kokarin tattalin Zaman Lafiya da kyautata Mu’amulan Zamantakewan ga hakuri da tawakkali da zumunci saboda haka muna kara kira gareshi da yacigaba da dukkan Halayensa na Alheri Allah Yakama.

Bayan tabbatar dashi Alhaji Sama’ilan a matsayin sarkin samarin Gomben yayi jawabin godiya ga mai martaba sarkin Gwamben da sauran ai’umar da suka bayar da gudummawa kamar haka.
Da Sunan Allah Ubangijin talikai, tsira da Aminci sukara tabbata ga fiyayyyen Halitta *Annabi Muhammadu (S.A.W)* Muna Mika Sokon Godiyan mu ta musamman ga Mai Martaba Sarkin Gombe Alh (Dr) Abubakar Shehu Abubakar III da ‘,Yan Majalisan Masarautan Gombe.
Allah Yasaka Masu da Alherinsa bisa Amincewansu agaremu

Muna Anfani da wannan daman muna godiya mara adadi bisa nuna mana Soyayya da Zumunci da akayi na samun karuwan arziki damuyi abun da muka gada na Arzikin Sarauta *Sarkin Samarin Gombe*
Lallai Mumga Soyayya kwarai musamman daga cikin gida da abokan mu na nesa masu Albarka inda muka samu addu’an ‘yan’uwa da mazumuntan mu
Muna kara mika Sakon Godiya da Bangajiya ga dukkan mahalarta wannan Bubban al’amari agaremu Mungode kwarai

Haka zalika muna kara godiya ga sauran jama’a da Sukayi mana addu’an da kuma wanda suka kiramu a waya Mungode kwarai Allah yaimaku sakayya da abinda yakema ma’abota zumunci Ameeeeeen

Allah Yaja Zamanin Sarki Amin
Anyi taro lafiya an tashi lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *