Daga Nasiru Adamu
Yau kimanin wata guda kenan da shuwagabanin Jam’iyar PDP gundumar Basawa karkashin jagorancin jajurtaccen danta kuma shugaban tsaretsare Jam’iyar PDP a karamar hukumar Sabon gari Hon Awwai Abdullahi Raba, suke ta karban bakuncin wasu daga cikin yayan Jam’iyar APC da suka canza sheka zuwa Jam’iyar PDP.
Wakilinmu ya sami halastan wasu daga cikin tarukan da Jam’iyar PDP ta gabatar, wanda ta karbi yayan Jam’iyar ta APC a emanam lokacin, ga kuma irin sakon da ya kalito mana
Ranar 5 ga watan 8 din da muke ciki kimanin mutum 580 akai bikin karbar su a makarantar Sá’idu primária dake cikin garin Samaru sanan ranar 14 ga watan akai bikin karban kimanin mutum 391 a cikin garin Basawa wanda shugaban su Hon Abubakar Muhammad ya jagorance Su,
Hakanan kuma ranar 27 da kuma 28 ga watan suka kara karban bakuncin mutum 650 aYardorawa da kuma 410 a Kasuwar yan gurguru dake Samaru karkashin jagorancin Alhaji Musa Kusada
Jim kadan bayan kammala wannan taron Alhaji Musa Kusada ya yiwa manema labarai karin haske akan dalilin canza shekar da yayan Jam’iyar APC ke yi zuwa Jam’iyar PDP sai ya ce. A gaskiyar magana bawani abu ke sa mutane canza sheka ba zuwa wannan Jam’iyar tamu illa wahalar da suke sha daga bakin mulkin da ake yi masu, kuma sunga cewar gwara mulkin PDP da wannan mulkin ta kowanne fanni ka dauka na rayuwa.
Daga karshe ya yi kira ga shaura, yayan Jam’iyar APC da su yi gaggawar fita Jam’iyar domin su zo cikin Jam’iyar PDP domin agudu tare a kuma tsira tare.