Daga Bello Hamza

Hukumar kula da iyakokin ruwan kasar da na hukumar kula da shige da ficen kasar nan sun sanya hannu akan yarjejeniyar aiki tare ta bangaren tantance takardun izinin shiga na kasa ga matafiya jiragen ruwa.

A sanarwar da ta samu sa hannun mataimakin darakta a sashin hulda da jama’a na hukumar NIMASA Mr Edward Osagie ta ce an cimma yarjejeniyar ne a lokacin da Shugaban hukumar shige da fice na kasa Mr Isah Idris Jere ya jagoranci manyan jami’an hukumar zuwa ziyarar aiki a shedikwatar NIMASA da ke birnin Ikko.

A jawabin Shugaban hukumar kula da iyakokin ruwan kasar nan Dr Bashir Yusuf Jamoh ya lura da cewa hukumar ta shige da fice na da rawar da za ta iya takawa wajen inganta tsaro a bangaren iyakokin ruwan kasar nan, a don haka, samar da takardun izinin shiga kasar nan ta hanyar jiragen ruwa ta hanyar manhajar zamani ya zama wajibi don ciyar da bangaren gaba.

A cewar Dr Bashir Jamoh, samar da tsaro a kan tudu tamkar samar da tsaro ne a bangaren iyakokin ruwan kasar nan, sannan ya bayyana aniyar hukumar wajen aiki tare da hukumar ta shige da fice don cimma manufar da aka sanya a gaba.

Ya kuma jaddada aniyar aiki tare da hukumar ta shige da fice wajen tantance kasashen asali na ma’aikatan jiragen ruwa da kuma tantance sahihancin takardun su na izinin shiga kasar nan.

Shugaban hukumar ta NIMASA ya kuma yaba da gudunmawar hukumar kula da shige da fice ke badawa a kokarinta na yaki da laifukan iyakokin ruwan kasar nan bisa tsarin doka, sannan ya nema cigaba da yaukaka dangantaka da hukumar.

A nashi tsokacin, Shugaban hukumar kula da shige da fice na kasa Mr Isah Idris Jere ya yabawa hukumar NIMASA bisa samar da manhajar adana bayanan ma’aikata na zamani a fadin kasar nan.

A cewar shi, ziyarar aikin wata manuniya ce na kyakkyawar alaqa tsakanin hukumomin biyu da zimmar yaki na kowane nau’i na laifuka a kan iyakokin ruwan kasar nan da kuma kare martabar ta.

Mr Isah Idris Jere ya kara da cewa samar da shaidar katin aiki na zamani ga ma’aikatan za taimaka matuqa wajen rage laifuka a tashoshin jiragen ruwan kasar nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *