Daga Umar Faruk Brinin Kebbi

Dakta Muhammad Zayyanu-Abdullahi Sarkin Yauri a jihar Kebbi, ya yaba da kokarin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Bihari na ci gaba da bunkasa  masarautar Yauri da ke a Jihar kebbi.

Ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin Manajan Darakta na National Inland Water Ways (NIWA) a ziyarar ban girma da ya kai a fadarsa da ke garin Yauri a karamar hukumar Yauri a jihar Kebbi.

Ya bayyana wasu ayyuka da gwamnatin shugaba Buhari ta aiwatar da suka hada da; gina hanyar da ta tashi daga Koko zuwa Yauri da hada Yauri tare da wasu kananan hukumomi tara tare da grid na kasa, layin KV 33.

Sauran ayyakan sun hada da ; kafa hukumar HYPADEC tare da nada dan asalin masarautar Yauri a matsayin shugaban hukumar, kafa masana’antar tumatur ta Ngaski da kuma kafa Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Yauri.

“Bana tunanin idan akwai wani wuri da Gwamnatin Tarayya ta nuna kasancewarta a Jihar Kebbi fiye da Yauri, don haka a madadin ni da Sanata Bala Ibn Na’Allah da Masarautarmu da daukacin al’ummar Yauri, ina son in kara mika  godiya ga Allah Madaukakin Sarki sannan kuma ga gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Bihari kan irin ci gaban da masarautar Yauri ta samu.

Haka zalika “Mun sha fama da ‘yan fashi da makami, amma a yau mun gode wa Allah, yanzu rundunar Sojoji ta girke jami’an ta  a nan kuma mutanenmu  suna  iya yin noma cikin kwanciyar hankali,” inji shi.

Da yake jawabi tun da farko, Manajan Daraktan NIWA, Dokta George Moghalu ya shaida wa Sarkin cewa, sun kasance a fadarsa ne domin neman alfarmar sarki, goyon baya da hadin kai don samun nasarar hukumar.

Haka Kuma ya tuna cewa yana daga cikin alkawuran da suka dauka na bude garin Yauri domin samun hanyar shiga kasar Mali har zuwa Bokinafaso ta hanyar safarar ruwa.

Sanata Na’Allah ya kuma tunatar da cewa, sun yi alkawarin gina tashar jirgin ruwa na zamani, inda ya tabbatar da cewa: “A yau za mu aza harsashin ginin a nan masarautar Yauri.

“Wannan tashar jirgin ruwa na zamani ne, inda duk fasinjojin da ke tafiya ta ruwa za su zauna cikin kwanciyar hankali, su shakata.  Sanatan  ya yi alkawarin ci gaba da yin duk mai yiwuwa don ganin an samu ci gaba mai kyau a masarautar Yauri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *