Daga Hussaini Ibrahim

Shehin Malamin Addini Musulimci a na Nigeriya, Jagoran Harkar Musulumci Shaikh Ibrahim Yakuba Al-Zakzaky (H) ya tura tawagar wakilansa,karkashi jagorancin Malam Nafiu, domin yin ta’aziyya gami da jajantawa ga iyalan marigayi Malam Sani Ra’is Funtuwa da ‘yan bindiga su ka yi wa kisan gilla a gidan sa da ke Funtuwa.

Wakilan Shiekh Zakzaky, Malam Nafiu, sami ganawa da Iyaye da iyalai da ‘yan uwan marigayi Malam Sani Ra’is, inda suka isar da sakon Jagora (H ) na ta’aziyyar kisan gillar da a kayi mi shi,  gami da jajantawa akan ‘ya’yan Marigayin guda biyu (2) da ‘yan ta’addan su ka tafi da su.

Da yake amsar gaisuwar,Kanin Mahaifiyar Malam Sani Rais, Malam Labiru Funtuwa,ya nuna matukar farin cikin su da ganin wannan tawaga mai albarka.kuma ya mika sakon godiya ga Shek Zakzaky da kuma sanya Iyalan Marigayi cikin addua dan kubutar da su daga hannan  ‘Yan bindiga.

Daga karshe wakilan sunyi Addu’a ga marigayin tare da fatan Allah (SWT) Ya gaggauta kubutar da ‘ya’yan marigayin daga hannun ‘yan ta’addan.

Adaren Juma’a ne  9/9/2022, ‘Yan bindigan su kaiwa Gidan Sani Muhammad Lawal Rais, marubuci kuma manomi dirarmikiya a Gidan sa da ke  Sabuwar Abuja cikin Karamar hukumar Funtuwa jihar Katsina , ‘yan bindigan sun nemi sutafi da shi Daji shi kuma yaki tafiya yayi iya kokarinsa wajan ganin ya turjemasu wannan ne ya sanya suka fito da shi bayan gida sa suka bude masa wuta suka kashe shi anan take .

Kisan Sani Rai’s Funtuwa da ‘Yan bindiga su kayi ya girgiza al’umma matuka mu samman masu bibiyar Rubutun sa da ya keyi na fagen Ilimin sanin Taurari da hisabi. da kuma kokarin bayyana ma Al’umma wanene Imamul Hujja (AJ).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *