Daga Ibrahim Muhammad Kano
Dan takarar majalisar tarayya na qaramar hukumar Fagge a jam’iyyar ADC Kwamared Haruna Kabiru Wakili ya jajantawa yan Kasuawar katin kwari bisa iftila’i da ya samesu na ambaliyar ruwa da jawo lalata dukiyoyi masu tarin yawa.
Ya kuma yi irin wannan jaje ga yan kasuwar Titin Bairut suma bisa matsalar da aka samu a kasuwar na rushewar wani gini da ya jawo asarar rai da raunata mutane.
Kwamared Haruna Wakili ya yi fatan wadanda abin ya shafa Allah ya mayar musu da alheri ya kuma bunkasa abinda aka rasa.
Dan takarar majalisar na tarayyar dai ya yi irin wannan jaje ga al’ummar yankin yan mata Gabas dake yankin Fagge bisa iftila’i na zaizayar kasa da ambaliyar ruwa daya shafe su da fatan Allah ya mayar musu da alkhairi ya kawo musu dauki na gaggawa kuma ya mayar da alkhairi ga dukkan al,’umma da ambsliyar ruwan ya shafa.
Kwamared Haruna ya yi kira ga mahukunta akan su kai dauki dan tallafawa wadanda sukayi asara, sannan a dauki matakai dan yin kandagarki ga aukuwar abin nan gaba.
Kwamared Haruna yace idan ya zama wakilin al’ummar Fagge a tarayya zai yi kokarin daukar matakan ganin an kyautata yanayin magudanan ruwa da kuma kawo dauki ga matsalar zaizayar kasa a wasu sassan yankin.