Daga Bello Hamza
Hukumar kula da iyakokin ruwan kasar nan-NIMASA ta bada tallafin kayayyakin karatu don inganta koyo da koyarwar ga dalibai dake matakin firamare a jihar Taraba.
Da yake miqa kayayyakin tallafin ga wadanda suka amfana a Jalingo, Shugaban hukumar, Dr Bashir Yusuf Jamoh yace kayayyakin tallafin na daga cikin muhimman kudirorin hukumar wajen ciyar da ilimin matakin firamare gaba.
Dr Bashir Yusuf Jamoh wanda wani jami’in hukumar-Kefas Kubuza William ya wakilta yace, hukumar har ila yau ta sayo kayayyakin kula da kula da lafiya a matakin farko a jihar.
Yace manufar rabon tallafin kayayyakin karatun da na kula da lafiya shine kyautata dangantaka da jihohi talatin da shida dake fadin kasar nan da kuma babban birnin tarayya, Abuja.
Dr Bashir Yusuf Jamoh ya kuma bukaci da ayi aiki da kayayyakin tallafin ta inda kowa da kowa zai amfana.
A nashi tsokacin, Darakta a hukumar bada agajin gaggawa na jihar Taraba, Mr Anthony Danu yace karancin kayayyakin koyo da koyarwa a makarantun gwamnatin jihar wata babbar barazana ce ga ilimi a matakin firamare a jihar.
Ya bayyana wasu daga cikin kayayyakin tallafin da suka samu da suka hada da na’ura mai kwakwalwa, allo na zamani, markers, takardun koyon karatu, kayayyakin rubutu, takardun rubutu, jakunkunan makaranta, takalman makaranta, safa da sauransu.
Shima a nashi tsokacin, daya daga cikin shugabannin makarantun da suka amfana, kuma shugaban makarantar Howai Primary School, Mallam Sa’ad Yakubu ya godewa hukumar ta NIMASA dangane da tallafawa bangaren ilimi, inda yayi nuni da cewa tallafin zai inganta koyo da koyarwa a makarantun nasu.
Ya kuma bada tabbacin yin amfani da kayayyakin yanda ya kamata wajen cigaban ilimi a jihar Taraba.
Wasu daga cikin kayayyakin kula da lafiya da hukumar ta bada tallafi sun hada da na’urar gwada dumin jiki, kayayyakin haihuwa, kayayyakin tsaftace hannu, zannunwan gadon asibiti da sauransu.