Daga Umar Idris Kaduna
Da safiyar ranar Talata ne kungiyar ci gaban Layin zomo dake karamar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna suka koka akan yadda garin nasu ya zama abin kyama ga yan siyasa bayan sun basu kuru’unsu a lokutan zabe.
Wakiliyarmu ta ziyarci Anguwar yayin da yan anguwar suka baiwa manema labarai goron gayyatar gani da ido a wannan yankin
Yayan kungiyan ta bakin shugaban su malam Danjuma Bawa sun bayyana cewa ya zuwa yanzu babu wani abin da zasu iya nunawa a matsayin romon Kamakuradiyya a halin yanzu.
Shugaban yace duk wani aikin da aka gani a yanzu to aikine da gwamnatin PDP tayi a lokacinulkinta na baya.
Tuni yayan kungiyar suka koka bisa irin kokarin da sukayi a wannan gwamnatin ta APC kafin run daga baya har zuwa yanzu.
Yayan kungiyar wanda galibinsu matasane masu jini ajika sun baiyana cewa yanzu haka akwai hanyoyi da suka lalace a tsakiyar garin Layin zomo amma babu wani dan siyasa da ya taba zuwa don kawo masu tallfin gyarawa.
Haka zalika matasa sunce yanzu haka kadar da ta hada garin Falladan da Layin Zomo itama ta lalace gaba daya.
Yayan kungiyar sun bayar da misali da makarantar UPE na Layin Zomon cewa yanzu haka awaki ne ke kwana a ciki sakamakon yadda ta lalace.
Sun kawo maganar Asibitin su dake anguwar shima sun koka da cewa ba kayan aiki ba magani kar yadda sauran takwarorinsu suke.
Karshe matasan sun nemi alfarma ga dukkan masu fada aji na karamar hukar Sabon gari da siyiwa Allah da Annabinsa su sa hannu akan halin da garin yake ciki a halin yanzu.
Kuma sunyi kira ga Dan majalisar taraiya Honorabul Garba Datti Babawo da ya waiwayi matasan yankin Layin Zomo a shirinsa daya saba gudanarwa lokaci bayan lokaci kamar yadda yake waiwayan sauran takwarorinsu dake fadin karamar hukumar ta Sabon Garin baki daya.
Malam Muhammad Mudassir shene sakataren kungiyar ta ci gaban Layin Zomon shima cewa yayi ya kamata yan siyasan karama hukumar Sabon Gari su gane cewa Layin Zomo ba abin yardawa bace domin sunada kuri’u masu yawa da yawansu na taka rawa sosai lokacin zabe bisa haka ne yace suna sane da duk Wanda ya taimaki yankin su to suma zasu taaka bashi a duklokacin daya zo neman nasu taimako.
Malam Zakari Sani tsohon shugaban yan Yan bangan Layin Zomo shiko cewa yayi gaskiya bai kamata ace sai dai jama’ar Layin Zomo suga anayin wasu aiyuka a wasu bangare su kuma suna gani.
Yace bisa haka yayi kira ga shugaban karamar hukuma da yan majalisarsu da suyi abin da ya kamata a wannan anguwa don haka ne zai karawa jambiyar APC farin jini tare da sumun nasara a nan gaban.
Karshe suyin fatan Allah ya kawo Wanda zai share masu hawayensu ba tare da sun wani matsalaba.