Daga Salisu Tukur Gaiwa

Masu iya magana na cewa mai son dan kwarai, ya auri isassa. Wannan falsafa daga kundin hikimomin Malam Bahaushe, ba ma za ta saidu kawai ba ne ga sauran al’ummomi. Har ma za a iya yin na’am da yabawa da ita. Domin kuwa duk inda ka ga dan kirki, daga kuma kowace irin al’umma ya fito, to kuwa babu shakka da ka bincika, za ka samu cewa ya samu tarbiya ta gari. Kaso mai tsoka kuwa na samun tarbiya tagari daga uwa ake samunsa. Domin kuwa ita ce ke tare da shi, take kuma kula tare da auna kowane irin motsi nasa tun daga kuruciya har girmansa.

Wannan ga kowane gama garin mutum kenan. Ga Alhaji dahiru Mangal, abin ya zarce haka. Domin kuwa yayarsa Hajiya Hauwa ta tabbatar mani da cewa alakar Alhaji dahiru Bara’u Mangal da mahaifiyarsa ta zarce duk yadda ake tsammani. Domin kuwa a kowace rana ta Allah, idan ya fito daga gidansa gidan mahaifiyarsa yake soma zuwa ya gaishe ta. Idan kuwa har wata hidima wadda ke da lokaci ta rutsa da shi, kamar daurin aure da makamancinsa, to kuwa idan ma har ya wuce bai samu zuwa ya gaishe ta ba, to kuwa daga can gidanta zai zarce. Haka kuma, idan ya yi tafiya ya dawo, gidanta yake soma zuwa kafin ya wuce gidansa. Sai dai ko idan da daddare ya dawo.

Ba gaisuwa kawai ke kai Alhaji dahiru Mangal ga mahaifiyarsa ba, har da sauraren bukatunta domin ya biya mata. Yana kuma jin linzaminta yadda ya kamata. Yana tsayawa cak, inda ta tsaida shi. Ya kuma ruga inda ta aike shi. Ma’ana dai bai hada ta da komai ba. Maganarta ita ce ta karshe. Kuma ko ya takura, huskarsa ba ta nuna takurar. Wasu na hasashen cewa wannan ne ma sirrin nasararsa. Ta yadda yake samun nasara ga dukkan abubuwan ya tunkara a rayuwa.

Malam Abbate wani dattijon Malami a garin Katsina wanda kuma ya rage daga cikin abokan Alhaji Bara’u wato Mahaifin Alhaji dahiru Mangal ya bayyana mani cewa Alhaji dahiru Mangal ya gaji wannan kyautatawa da yake yi wa Mahaifiyar tasa ne daga Kakansa Alhaji Tukur wanda yakan je ya gaida mahaifiyarsa wadda ake cewa Done a kowace rana. Malam Abbate ya kara da cewa “Shi ma Mahaifinsa Alhaji Bara’u yakan zo gaishe da wannan tsohuwa da kuma kawo mata abinci. Ta haka ne ma muka saba da juna har muka zama aminan juna da yake gidanta yana makwabtaka da gidanmu. Don haka, duk lokacin da ya zo yakan shiga ya gaishe da Shehi (Mahaifinsu).”

An haifi Hajiya Murja Muhammad Dodo a shekarar 1937. Mahaifinta shi ne Alhaji Dodon Kanti. Ita ce diyarsa ta biyu. Ta yi aure tun tana da shekara goma sha ukku (13), a duniya, a shekarar 1950. Ta haifi ‘ya’ya takwas, hudu maza, hudu mata. Mazan su ne Alhaji dahiru Bara’u Mangal (na farko a cikin maza, na biyu a haihuwa) da Marigayi Alhaji Muntari da Alhaji Bishir da kuma Marigayi Alhaji Marwana. A lokacin da matan suka kasance Hajiya Hauwa (ta farko a haihuwa) da Marigayiya Hajiya Mariya da Hajiya Zulai da kuma Marigayiya Hajiya Nana Bilkisu.

Aminiyar Hajiya Murja, wadda suka taso tare mai suna Hajiya …, wadda aka fi kira da Hajiya ‘Yarbaba, ta sheda wa Mujallar Damina cewa ko a lokacin kuriciyarsu, Hajiya Murja ba ta zuwa dandali, kamar yadda sauran ‘yan mata suka saba a bisa al’adar Hausawa, saboda tarbiyyar gidansu. Da kuma kasancewar ta fito daga gidan wadata. Ta kuma ce a duk shekara sau ukku take kaita Makka, sau biyu umra, sai kuma aikin Hajji. An kuma jera haka har sau shekaru goma sha biyar. Har zuwa lokacin da ta kasa zuwa saboda ciwon kafa. Banda ita kuma tana daukar dawainiyar tafiyar wadansu ma. Kuma dukkan nauyi take daukewa ba tare da rage komai ga wanda ta dauki nauyinsa.

Marubucin wannan mukala ya jinjina masa a lokacin da wani abokinsa Alhaji Magaji Abdullahi Kankiya ya sheda masa cewa a lokacin da ya je aikin Hajji sun zo filin jirgi za su dawo gida a jirgin Max Air sai suka iske Hajiya (mahaifiyar Alhaji dahiru Mangal) ta riga ta shiga jirgin ita ma za a dawo da ita. Irin yadda ya ga gabaki dayan ma’aikatan jirgin na kazar-kazar da ~arin jikin ganin fasinjojin jirgin su shiga jirgin a cikin gaugawa, domin kada a ~ata wa lokaci. Lamarin da ya sa Alhaji Magajin ya sheda irin tsabar girmamawar da Alhaji dahiru Mangal ke yi wa mahaifiyarsa. Wanda kuma ga shi har hakan ya yi naso ga ma’aikatansa.

Allah Ya jikanta. Ya girmama lada. Ya kuma sa jannatul firdausi ta zama makomarta.

 

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *