Daga Bello Hamza, Abuja

Ministanharkokin sufuri Alhaji Mu’azu Jaji Sambo ya yabawa hukumar kula da iyakokin ruwan kasar nan dangane da kawo cigaba da sauye-sauye masu ma’ana a bangaren harkokin iyakokin ruwan kasar nan.

Ministan yayi yabon ne a lokacin da ya jagoranci tawaga ta musamman na ma’aikatar shi zuwa ziyarar aiki a shedikwatar hukumar NIMASA dake birnin Ikko.

Alhaji Mu’azu Jaji Sambo ya kuma bayyana gamsuwar shi bisa yanda NIMASA take inganta kwazon matasan kasar nan ta hanyar karawa juna sani kamar gasar kacici-kacici a makarantun gaba da sakandare.

Ministan ya jaddada aniyar ma’aikatar wajen aiki tare da NIMASA don inganta sufurin jiragen ruwa da zimmar habbaka bangaren sufurin jiragen ruwan kasar nan.

Alhaji Mu’azu Jaji Sambo ya kuma bukaci NIMASA da tayi aiki tare da sauran ma’aikatun dake karkashin kulawar ma’aikatar da kuma rundunar sojin ruwa da kuma rundunar tsaron kasa don cimma manufar da aka sanya a gaba.

A nashi jawabin, Shugaban hukumar kula da iyakokin ruwan kasar nan, Dr Bashir Yusuf Jamoh ya yabawa Ministan bisa jagorancin shi abin koyi, sannan ya bada tabbatar da cigaba da aiki bisa tsarin doka don inganta bangaren iyakokin ruwan kasar nan.

Shugaban hukumar ya kuma bayyanawa Ministan irin nasarorin da hukumar ta samu don tafiyar da ita daidai da zamani.

Ya kara da cewa hukumar na cigaba da horas da ma’aikatanta da kuma hadin gwiwa da hukumomin tsaro don kare iyakokin ruwan kasar nan daga mabarnata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *