Daga Nasiru Adamu
Ranar Lahadin karshen makon da ya gabata kungiyar”LAJNATU MADARISIL ISLAMIYYAH” ta gabatar da bikin gasar musabakan karatun Alkur’ani da ya gudana a tsakanin Makarantun Islamiya daban daban dake gundumar Basawa a cikin karamar hukumar Sabon gari.
Taron wanda aka yi shi a cikin Babban Masallacin Kasuwar Samaru, ya sami halastan Manyan Malamai da shuwagabanin Siyasa, tare da daliban makarantun Islamiyoyi cikin garin Samaru da kewaye.
A lokacin wannan taron shugaban Malaman gungiyar Izala reshen Sabon gari, Shek Farfesa Sa’idu Yunusa, wanda kuma shine babban bako mai kawaii, ya jawo hankalin daliban da suka zamto zakakurai a wannan gasar, da kar su kasance masu alfahari akan nasarorin da Allah ya basu, wajen nuna tunkaho ga abokan gasar su, da jin sun fi kowa.
Hakanan wadanda basu sami nasara ba, kar wannan ya sanya, sanadiyar nuna gaba da kiyayya ga wani, ko ya zamto sanadin karya masu kwarin gwiwar a nan gaba.
Hakanan shima, anashi jawabin da ya gabatar, Shugaban kungiyar shirya wannan Musabakar, Malam Muhammad Awwal Má’ahd, ya bayyanawa manema labarai dalilin wannan shirin musabakar da suke yi wa dalibai, shine domin zaburantar da su, wajen kara bada himma akan darusan da ake yi masu a makarantun su, da kuma janyo hankalin sauran yaran da basa zuwa makaranta su sami azamar zuwa. .
Malam Awwal ya bayyana Makarantun da suka sami shiga wannan gasar sun kai kimanin guda 25, sannan Makarantun da suka zamto zakaru a wannan gasar, sun hada da “Makarantar Mu’azu bin Jabal” da ke Hayin dogo Samaru, da Al-Makka Academy Samaru da kuma a “Makarantar Markaz Palladan” Zariya.
Daga karshe ya jawo hankalin iyaye da su ringa baiwa Malamai goyon baya wajen hada kai da su, domin samar da kyakkyawar tarbiya irin na Addinin musulunci.