Daga Nasiru Adamu
A makon da ya gabata ne kungiyar Matasa dake layi tsamiya Hayin dogo Samaru, wadda ake yi wa lakabi da “Tsamiya Youth Moltipupose Co-oporatives” ta bukaci al-umma da su kasance masu son zaman lafiya da kaunan juna a tsakanin su.
Wannan jawabin ya fitone daga bakin Shugaban kungiyar kwamred Shamsudden Usman, a lokacin da yake jawabi wajen kaddamar da sabon ofishin kungiyar dake kan titin yar tsamiya Hayin dogo Samaru
Haka nan ya ce babban manufar wannan kungiyar ta su shine hada kan Alumma guri daya da kuma basu shawarwari domin ci gaban su na yau da kullum.
Komred Shamsudden bai tsaya nan ba ya ci gaba da cewar wannan kungiyar tana gudanar da aikin gayya domin taimakon al’umma .
Daga karshe ya bukaci hadinkan al’umma, tare da ba kungiyar tasu goyon baya, domin ganin ta samu kafuwa daram a wannan yankin, don cimma manifofinta.