Daga Nasiru Adamu

A Wata tattaunaw da manema labarai suka yi da babban manajan Kamfanin 5G dake daura da get din “Energy research” dake Jami’ar Ahmadu Bello samarun Zariya Malam Jibrin Salisu ya bayyana cewar, sun bude wannan babban Ma’aikatan mai suna 5G sakamakon samar da aikin yi ga matasan yankin lardin Zazzau.

Hakanan Malam Salisu, ya ce baya ga samar da aikin yi ga matasan, wannan kamfanin wurine na nishadi da wasanni ga kananan yara damin kara masu kaifin kwakwalwa da basira.

Sannan kuma ya ce wannan kamfanin bai takaitu akan hakaba kadai, ya tanaji dadadan abinci da ababen tande tande da lashe lashe daban daban, har da shaye shaye masu gamsarwa ga mazauna da Matafiya

Daga karshe ya ce a halin yanzu wannan Kamfanin yasami nasaran daukan Matasa Maza da Mata kimanin mutum 30, kuma zai ci gaba da dauka da Izinin Allah dazaran sun kammala bangaren cin abinci da wuraren mutsa jiki, nan bada dadewa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *