Daga Bello Hamza
Sashin iyakokin ruwan kasar Amurka ta yaba da kokarin da Nijeriya take yi wajen dakile ayyukan mabarnata a kan iyakokin ruwan ta, har da na tafkin guinea.
A sanarwar da mataimakin darakta a sashin hulda da jama’a na hukumar kula da iyakokin ruwan kasar nan-NIMASA, Mr Edward Osagie ya rabawa manema labarai a birnin Ikko ya ce jinjinan ya fito ne daga bakin kaftin Brian Lisko a lokacin da ya jagoranci ayari daga sashin kula da iyakokin ruwan kasar Amurka zuwa shedikwatar hukumar NIMASA dake birnin Ikko.
Kaftin Brian Lisko ya kuma yaba da rawar da NIMASA ta taka wajen hadin gwiwa don tabbatar da tsaro a tafkin guinea, inda ya ce kasar Amurka na sha’awar inganta hadin gwiwa da NIMASA da sauran hukumomi wajen dorewar wannan nasara akan iyakokin ruwan Nijeriya.
Kaftin Brian Lisko ya bayyana cewa Amurka na shirin aiko da mashawarci na musamman akan iyakokin ruwa da zai dinga bada shawarwari kan yanda za a samar da kwararrun da za su taimakawa NIMASA.
Kaftin Lisko yayi nuni da cewa babban burin sashin kula da iyakokin ruwan kasar Amurka shine taimakawa abokan huldar ta ta fuskar kula da gudanar da tashoshin jiragen ruwa, inda yace sun zo Nijeriya ne don ganawa da masu ruwa da tsaki a fannin kula da iyakokin ruwan Nijeriya saboda matsayin da hukumar NIMASA take da shi a idon kasar ta Amurka.
Da yake jawabi, Shugaban hukumar NIMASA, Dr Bashir Yusuf Jamoh ya lura da cewa wakilan sashin kula da iyakokin ruwan kasar Amurka sun ziyarci Nijeriya da dama a shekarun da suka gabata a matsayin abokan hulda, inda ya bukaci karin hulda ta fuskar samar da kwarewa da yin aiki tare.
Ya bayyana godiyar hukumar dangane da goyon bayan da hukumar take samu daga kasar Amurka, inda yayi nuni da cewa wannan ziyara ta zo a daidai kan gaba.
Dr Bashir Jamoh ya tuno da cewa a shekarun da suka gabata, sashin kula da iyakokin ruwan kasar Amurka ta taba kawo ziyara a hukumar don yin nazari akan tashoshin jiragen ruwan kasar nan da kuma jiragen ruwa don duba ingancin su, sannan ya bukaci da su cigaba da kawo irin wadancan ziyara da kuma bada gudunmawa wajen samar da kwararrun shawarwari.