EFCC TA SHAWARCI MUTANE SU DAINA AMFANI DA LAMBAR WAYAR DA SUKE AMSAR SAKONNIN BANKI A SOSHIYA MIDIYA

Daga Mansur Aliyu

Shugaban hukumar EFCC ta kasa reshen jihar Kano, Mr.Dogondaji M. Farouk, shi ne ya yi wannan gargadi lokacin da shugaban makarantar Sakandaren gwamnatin tarayya ta Kano, (FGC), wato Alhaji Ibrahim Uba ya kai ma hukumar ziyarar ban girma a ofishinsu dake Kano.

Shugaban hukumar ya ce, ‘yan danfara da aka fi sani da yan Yahoo sukan wawushe kudaden jama’a ta bin diddigin lambobin wayoyin da suke anfani da su musamman a bankuna a hanyoyin sadarwa irinsu Whatsapp, Facebook, ko Gmail da dai sauransu. Inda ya ce suna samun korafe korafen yadda ake kwashe kudaden jama’a daga bankuna ta irin wannan hanyar.

Ya jawo hankulan jama’a da su daina anfani da dukkan wata lambar wayar da mutum ke samun sako (alert) daga bankuna a duk wata kafar sadarwa, saidai in har ya zama dole to ka sami karamar wayar hannu wacce ba android ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *