Daga Ibrahim Muhammad Kano
Hukumar Kidaya ta Kasa zata dauki ma’aikata na wucin gadi samada miliyan guda da zasuyi aikin kidaya a badi a qasarnan.Shugaban hukumar ta qasa Nasir Isah kwarra ne ya bayyana hakan a yayin qaddamarda daukar ma’aikata ta yin amfani da na’ura mai kwakwalwa na wadanda za suyi kidaya da gidaje da akayi a jihar Kano.
Shugaban hukumar na kasa Wanda kwamishinan hukumar kidaya na tarayya na jihar Kano Dokta Isma’ila Lawan Sulaiman ya yi bayani a madadinsa yace daga buxe shafin an sami mutane Samara 200,000 suka nemi aikin
Yace a neman aikin jihohi hudu ne akan gaba da suka hada da Kano.Nasarawa,Katsina da Kaduna.Wanda a jihar Kano suke sa ran daukar ma’aikata 100,000 Kuma shafin neman aikin wucin gadin na hukumar zai cigaba da zama a bufe har zuwa karshen shekarannan.
Dokta Ismaili’ Lawan yace masu buqata ta musamnan da ma’aikata da wadanda ba ma’aikata na daga cikin wadanda zasu iya neman aikin ya kuma yi kira ga al’ummar jihar Kano suyi amfani da wannan shafin dan neman aikin.kuma hukumar zata gudanarda wayar dakan al’umma ta fannoni daban-daban dan nuna musu muhimmancin kidayar.