Daga Ibrahim Muhammad Kano
An bayyana cewa lalacewar  gini ba kawai rushewar sa bane kawai illa ta farko domin kafimma ya ruguje akwai lalacewarsa,Wanda yasan gini shi zai gane ginin na cikin matsala amma karshen lalacewar gini shine ya rushe. Shugaban kungiyar Injiniyoyi na kasa.Injiniya  Tasi’u Sa’ad Gidari Wudil ya bayyana hakan da yake zantawa da manema labarai a yayin kaddamarda Shugaban Kungiyar reshen jihar Kano.
Yace masu harkar gini ba injiyoyi ne  akwai ba,akwai masu yin zane da masu tantance yawan abubuwanda za asa a wannan ginin da magina, sannan injiniyoyi,amma ko yaushe in gini ya lalace sai ace injiniya.
Yace shi Injiniya shine keyin  ginshikin gini saboda haka in gini ya rushe Wanda ya yi ginshikin gini,shi za’a zarga. Amma shi wanda yasa ayi ginin yasa Injiniya a ciki?Saboda mutane na ganin kamar bata kudin sune in suka kira
 Injiniya.Sai sai  zasu zuba miliyoyin kudi suyi gini ba tareda Injiniya ba.
Shugaban Injiniyoyin na kasa.Injiniya Tasi’u Sa’ad yace wasu ma Injiniya zai zo ya zana musu komai bayan ya zana sai su zage su dauko wani da ba Injiniya ba, ya lura da ginin sai a ciccire abubuwa daga ciki  ayi ginin sai a karshe ginin ya lalace ko kuma ya rushe.
Yace in kanaso ka sami gini a tsare a yanda  zaka tabbatar gininka ba zai rushe ba,shine a wajen zanen ginin ka hada da  injiniya a wajen yanda za’a lura da ginin har a kammalashi tun daga farko har karshe kasa injiniya.Amma sai ya zama Kudinda za’a baiwa wannan injiniya shine mutane ke jin kyashin bayarwa kuma in kayi kyashin bayarwa zaka taras gininka ya lalace ko kuma ya rushe.
Injiniya Tasi’u Sa’ad ya yi kira ga sabbin shugabannin Injiniyoyin na kasa reshen jihar Kano da aka kaddamar akan suyi aiki bisa gaskiya dan kare martabar aikinsu.
Shima a nasa bangaren da yake zantawa da yan jarida sabon Shugaban kungiyar Injiniyoyin na kasa reshen jihar Kano.Injiniya Ibrahim Dederi ya yi kira Usman  ga Injiniyoyi dake Kano su fito su basu hadin kai da goyon baya, sannan su kuma zasu cigaba da gudanarda aiki kafada da kafada da Gwannati a dukkan ayyukan gine-gine da ake aiwatarwa a Kano anyi su yanda yakamata.
Yace sunada kalubale da yawa. ta fannoni daban-daban in aka dauki matsala ta rugujewar gini da ake fama dashi babban kulensu shine, nasu Kansu al’umma wanda yakamata su canza daga zuwa su nemi wadanda ba kwararrun Injiniyoyi ba,su nemi Injiniyoyi na hakika kuma in sunaso su sami na hakika suzo wajen kungiyar zasu nuna musu.
Yace mutane da suke kaucewa mu’amala ta gini ta kin zuwa ga Injiniyoyi saboda gudun kashe kudi da yawa  araha da suke bi kan zama batayi musu ado ba domin daga karshe sai suzo su jawo abinda za’ayi asara koma a rasa rayuka Allah ya kiyaye.
Injiniya Ibrahim Usman Dederi ya yi kira ga Injiniyoyi a duk inda suke su cigaba da jajircewa wajen aikinsu su tabbatar sun rike  amana duk inda suke.
Pic.Injiniya Ibrahim Usman Dederi.Shugaban Kungiyar Injiniyoyi na jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *