Daga Bello Hamza
Babban Sakataren hukumar kula da iyakokin ruwa na duniya, Mr Kitack Lim zai ziyarci Nijeriya daga ranar ashirin zuwa ashirin da biyu na wannan wata don halartar taron karawa juna sani a bangaren iyakokin ruwa.
A sanarwar da mataimakin darakta a sashin hulda da jama’a na hukumar NIMASA Mr Edward Osagie ya fitar ya ce ma’aikatar sufuri da hukumomin dake karkashinta ne suka shirya taron.
A cewar Ministan Sufuri, Injiniya Mu’azu Sambo yace a shirye gwamnatin tarayya take wajen samar da kyakkyawar yanayi ga masu ruwa da tsaki a bangaren iyakokin ruwa don cimma manufar da aka sanya a gaba.
A nashi tsokacin, Shugaban hukumar kula da iyakokin ruwan kasar nan, Dr Bashir Yusuf Jamoh yace wannan ziyara ta Mr Kitack Lim wanda itace karo na farko a shekaru goma sha biyar da suka gabata, wata manuniya ce dake nuna karbuwar Nijeriya a idon duniya.
Yayi nuni da cewa Nijeriya zata cigaba da inganta bangarenta na iyakokin ruwa har sai ta shiga sahu na farko a fadin duniya.
A cewar Mr Emeka Akabogu, taron na karawa juna sani wata dama ce ta tattauna batutuwan da suka shafi bangaren a aikace da nufin samar da hanyoyin magance kalubalen dake fuskantar bangaren.
Ana sa ran Mr Kitack Lim zai ziyarci hukumar NIMASA don ganewa idon shi yanda take gudanar da ayyukanta kasancewar ta itace hukuma daya tilo a karkashin ma’aikatar sufuri dake da alaqa da hukumar kula da iyakokin ruwa na duniya.