A Najeriya,  wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da masallata 19 bayan harbe limamin a wani hari da suka kai wani masallaci a jihar Katsina.

Kakakin ‘yan sandan jihar Katsina Gambo Isa ya ce Maharan sun far wa masallacin ne da ke kauyen Maigamji a jihar lokacin sallar magariba da yammacin Asabar, inda suka yi garkuwa da mutanen bayan sun harbe limamin tare da raunata wani mai ibada.

Gambo Isa ya ci gaba da cewa jami’an ‘yan sanda sun bi sawun wadannan ‘yan bindiga, kuma sun yi nasarar kubuto 6 daga cikinsu daga barayin, a yayin da ake ci gaba da kokakrin karbo saura 13 da sukaa rage.

Arewa maso yammaci da kuma maso tsakiyar Najeriya na fama da ayyukan masu aikata manyan laifuka da ake kira ‘yan bindiga, wadanda suke kai samame kauyuka, suna satar mutane da shanu don karbar kudin fansa, suna kuma kona gidaje bayan sun kwashe abubuwan da ke ciki.

A watan da ya gabata, mutane 15 ne ‘yan bindiga suka kashe, suka kuma raunata da dama a jerin hare haren da suka kai wasu kauyuka a jihar Kaduna da ke makwaftaka da Katsinar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *