Daga Shu’aibu ibrahim Gusau

Rundunar ‘yan sandar jihar Zamfara ta kama wasu da ake tuhuma da laifin hada baki da ‘yanbindiga Safaran miyagun kwayoyi, da busasshen ganyen tabar wiwi.

Hakan na kunshe ne a cikin wata takarda wanda jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu ya sanya wa hannu aka rabata ga manema labarai a Gusau.

Takardar na cewa an kama wadanda ake zargin Murtala Dahiru mai shekaru 25 dake kauyen Galadi da ke karamar hukumar Shinkafi da Sani Mohammed mai shekaru 39 dake karamar hukumar Talata Mafara, yayin da suke jigilar ganyen tabar wiwi da ake zargin an daukosu daga Legas ke Zamfara.

Shehu ya kara da cewa, a yayin da ake gudanar da bincike, wadanda ake zargin sun amince da samar da magunguna masu tsauri da sauran abubuwa ga ‘yan bindigar da ke aiki a yankin Shinkafi da Zurmi.

Ya Kara da cewa, an kama wasu mutane biyu da ake zargin ‘yan fashi ne, Masu hada kai da ‘yan bindiga, wadanda suka hada da, Abubakar Idaho mai shekaru 75 dake kauyen Kwarya Tsugunne a karamar hukumar Maru,da Almustapha Dahiru mai shekaru 69 dake kauyen Yanbuki a karamar hukumar Zurmi, da Mohammed Sani Jibrin na kauyen Kekun Waje a cikin Bungudu LGA.

Muhammad Shehu ya ce, jami’an ‘yan sanda sun kama mutanen biyu da ake zargi da laifin hada kai da ‘yan bindiga domin sanya haraji a kauyukan Kwarya Tsugunne da Yanbuki da ke karamar hukumar Maru da Zurmi.

Ya ce“Wadanda ake zargin a lokacin da ake yi musu tambayoyi sun shaida wa ‘yan sanda cewa, a lokuta da dama, sun sanya haraji kan mazauna kauyukan da suka kai miliyoyi .

“Yayin da aka kama wanda ake zargin na 3 a matsayin mai yiwa ‘yan bindiga bayanai ta hanyar bayyana ayyukan jami’an tsaro da ‘yan banga a kauyen Kekun Waje a karamar hukumar Bungudu. Wanda ake zargin yayin da ake yi masa tambayoyi ya amsa laifin da ake zarginsa da shi”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *