SHUGABA BUHARI YA AMINCE DA BAIWA ‘YAN NIJERIYA RANCEN KUDADE DON MALLAKAR JIRAGEN RUWA
Daga Bello Hamza
A kudirinta na ganin yan Nijeriya sun mallaki jiragen ruwa cikin sauqi, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da gagauta bada bashi ga yan kasa masu ra’ayin mallakar jiragen ruwa.
Ministan harkokin sufuri, Injiniya Mu’azu Jaji Sambo ne ya bayyana haka a wajen taron manema labarai inda ya ce an amincewa bankunan Union, Zenith, Polaris, UBA da Ja’iz a matsayin cibiyoyin da za su rarraba kudaden.
Ministan yayi nuni da cewa ma’aikatar shi ta fara tuntubar Ministar kudi, da Gwamnan babban bankin Nijeriya don fara aiwatar da tsarin.
Ya kuma bayyana fatan cewa wannan tsarin zai kara bunkasa hada-hadar sufurin jiragen ruwa a bangaren iyakokin ruwan kasar nan.
A nashi tsokacin Shugaban hukumar kula da iyakokin ruwan kasar nan, Dr Bashir Yusuf Jamoh yayi bayanin cewa kudaden da aka amince a bada rance sun haura sama da naira miliyan dubu goma sha shida, sai kuma kimanin dala miliyan dari uku da hamsin.
Shi dai wannan tsarin an fara shi ne a shekarar 2003 don karfafawa gwiwar yan Nijeriya su mallaki jiragen ruwa don gudanar da kasuwanci inda za su biya kashi goma sha biyar, ita kuma hukumar NIMASA ta bada kashi talatin da biyar, sai kuma bankuna su bada kashi hamsin.