Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

A Larabar da ta gabata ne Jam’iyar APC ta kaddamar da sabbin shugabannin a matsayin masu yakin neman zaben Bola Ahmad Tinubu a matsayin shugaban kasa mai zuwa a 2023. Wannan yana dauke ne cikin wata tadarda Mai dauke da sa hannun mataimakin sakataren yada labarai na ofishin kodineta na jiha, Idris Salisu.

Da yake jawabi ga sabbin shugabannin, ko’odineta na Jihar, Alh Tanimu Mada ya ce zabar su ya samo asali ne daga irin ayyukan da suka yi da kuma sadaukar da kai ga jam’iyyar APC ta jihar, ya ce yanzu za ku jajirce wajen yin aiki don ganin Bola Ahmed Tinubu ya samu mafi yawan kuri’u domin tabbatar da shi a matsayin shugaban Najeriya kuma Gwamna Bello Mohammed Matawalle ya dawo a matsayin gwamnan jihar a 2023.

Ya ce “Ina kira gare ku yi aiki tare a matsayin kungiya don ganin Bola Ahmad Tinubu da Kashim Shattima su zo a matsayin shugaban kasa da mataimakin shugaban kasar Tarayyar Najeriya”.

Da yake bayyana abin da shuwagabannin ya kamata suyi don tabbatar da cigaban wa’adin mulkin APC a Zamfara da kasa Baki Daya , Tanimu Mada ya bayyana cewa su himmatu wajen zaburar da jama’a tun daga matakin jiha har zuwa mazabun kananan hukumomi 14 na jihar.

Shima da yake jawabi sakataren jaha , Kwamared Mansur Mustapha ya yaba da kokarin da Jam’iyar reshen jihar ke yi wajen ganin an kaddamar da sabbin mambobin Yakin Neman zaben.

Ya kara da cewa, Tinubu yana da dukkan karfin da zai iya kai Najeriya mataki na gaba, a cewarsa Tinubu a matsayinsa na dan dimokuradiyya na gaske wanda ya yi aiki a wurare daban-daban musamman a matsayin wanda ya sauya jihar Legas a matsayin Gwamna da kuma irin gudunmawar da ya bayar wajen gina kasa, inda ya ba da tabbacin cewa idan har ya zama shugaban kasar Najeriya a shekarar 2023, ‘yan Najeriya za su ji dadin zabensa a matsayin shugaban kasa.

Don haka Kwamared Mansur ya yi kira ga sabbin shugabannin da su farka su yi dabara a kowane mataki don tabbatar da nasarar Jam’iyar, ya kara da cewa za a yi amfani da tsarin yakin neman zabe na gida-gida a fadin jihar, sannan ya bukace su da su dauki bikin kaddamarwar a matsayin hanyar da ta dace ta zaburar da su don yin yaki a zaben da ke gabatowa na 2023″

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *