Daga Abubakar M Taheer
Babban Jam’iyyar hamayya ta PDP ta Nuna Rashin jin dadinta cike Allo Mai dauke da sunan Atiku da Yan Jam’iyyar APC sukayi a Taron da suka gabatar jiya Lahadi.
Haka na ciki wata tattaunawa da Shugaban matasan Jam’iyyar Umar Dan Jani yayi da wakilin mu a wayar tarho.
Umar DanJani Yana matukar damuwarsa Kan sakacin Jamian tsaro inda ya bukaci a gaggauta zakulo Wanda suka aikata haka.
Dan jani ya Kara da cewa idan ya zama hukumomin tsaro basa daukar matakin Kan masu aikata irin wanna laifi zai zama barazana ga zaman lafiyar jihar Jigawa dama Hadejia baki daya.
Haka Kuma Umar Danjani ya Kara da cewa irin wannan halayya ta Jam’iyyar APC tasa bazasu Kara komawa a shekarar 2023 ba.
Rundunar Yan sanda a jihar Jigawa ta bayyana cewa ta baza komarta domin zakulo masu hannu a Wannan aika-aika.
Cikin satin daya gabata ne Dan Takarar Shugaban kasa Na Jam’iyyar PDP ya ziyarci garin Hadejia domin jajantamusu Kan ambaliyar ruwa.
Inda Dan Takarar ya bada tallafin naira miliyan hamsin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *