Daga Ibrahim Muhammad Kano
Cibiyar Nazarin Damakwaradiyya ta Malam Aminu Kano dake karkashin jami’ar Bayero ta kaddamarda littafi akan tarihin marigayi Furofesa Haruna Wakili.
Taron Wanda aka gudanar dashi a dakin taro na cibiyar karkashin jagorancin tsohon Gwamnna jihar Jigawa.Alhaji Sule Lamido ya sami halartar dinbin mutane da suka had a da shehunnan malamai na jami’a da sukayi aiki da marigayin tareda dalibansa da yan’uwa da abokan arziki.
Tsohon Gwamnan na.Jigawa Sule Lamido ya yi bayani sosai akan halayya da mutuntaka da rawarda Marigayi Haruna Wakili ya taka a wajen cigaban ilimi da jihar Jigawa.
Sannan ya yaba da yanda taron ya gudana tareda nuni da cewa ba’a taba yin taro a dukkan tarukanda cibiyar Damakwaradiyyar ta yi ba, da ya yi armashi kamar wannan da mutanenda suka halarta basu zaku su tafi ba.In aka kwatanta da tarukanda ake da mutane kan rika tafiya kafin a gama.
Sannan sai ya yi kira ga shugabannin cibiyar su rika gudanarda tarukansu da harshen Hausa hakan shine mafi saukin kai sakonda akeso a tura ga mahalarta taron bada turanci da ake yawan yi ba.
Dokta Akilu Sani Indabawa shine ya gabatarda nazari littafin da kuma yabawa da yanda akayi littafin duk kuwa da cewa akwai wasu bangarori da dama da ba’a ma kai ga rubutasu a littafin ba, gameda rayuwar Haruna Wakili.
Alhaji Sule Lamido yace yana daga nasarar da aka samu taron yadauki hankalin jama’a suka tsaya, suka saurara saboda yinsa da akayi da Hausa.Ya godewa mahalarta taron da kuma addu’ar Allah ya jikan Haruna Wakili.
Jama’a da dama ne suka gabatarda jawabai akan kyawawan halaye da irin gudummuwa da marigayi Haruna Wakili ya bayar ga cigaban al’umma a fannnoni daban-daban.
Taron kaddamarda Littafin ya sami halartar babban mai kaddamarda littafin.Alhaji Bashir Dattahatu da shugaban kamfanin H&M.Alhaji Muhammad Hassan Yakasai da sauran mutane da dama da suka bada gudummuwa a kaddamarda littafin.