Daga Muhammad Sakafa, Kano
msakafa@gmail.com
A ranar Asabar da ta gabata ne dandamalin zuba hannun jari mai suna ‘MAKOMARMU INVESTMENT AND CREDIT CO-OPERATIVE SOCIETY LIMITED’ ya gabatar da taronsa na shekara shekara (AGM) don sanin abubuwan da dandamalin ke ciki da inda aka kwana.
Sakataren kungiyar Alh. Bashir Bala, ya karanto nasarorin da aka samu tare da matslolin da aka fuskanta, sannan sai sakataren kudi Malam Zakariyya, kaduna, yayi dan takaitaccen jawabi kan yadda aka tattara hannun jarin tare da ribar da aka samu kan kowanne hannun jari.
Daga busani mataimakin shugaba mai kula da zuba hannun jari wato Dr. Nasir Ja’afar daga jihar zamfara, inda yayi nasa jawabin kan yadda ake zuba hannun jari da kuma mafi karancin siyen hannun jari guda daya.
A nasa jawabin da kuma hirar da yayi da manema labarai shugaban tafiyar Alh Kabiru Adamu Auduwa, ya fadi makasudin kafa dandamalin inda yace “an kafa wannan dandamalin ne na zuba hannun jari saboda habaka tattalin arzikinmu dana iyalanmu dama wadanda suka amince zamu tafi tare a wannan bangaren.
A bangaren nasarori an sami nasarori da dama ta hanyar yin wani Abu da wasu ke ganin ba zai yiwu ba, ta inda muka tara al’umma mai taro mai sisi don juyawa a sami riba, sannan bamu gajiya ba duk da kalubalen da muke samu an ci gaba, ta inda muka tattara akalla hannun jari dari da sha biyar (115) gashi yanzu mun zo don taron shekara na raba riba ga dukkan mai hannun jari ciki daga daya zuwa sama.”
Alh kabiru Adamu yayi kira ga dukkan masu son zuba hannun jarinsu cikin wannan dandamalin da cewa “dukkan mai son zuba hannun jari a cikin wannan tafiya musamman masu kananan jari da manyasu da su zo su sayi hannun jarin don kofarmu a bude take babu ranar rufewa a wannan karon, kuma muna tafiya ne da zamani ta yadda ko daga ina kake a fadin duniyar nan zaka iya yankar fom dinmu tare da siyan hannun jarinka, sannan a shirye muke wajen bunkasa masu kananan sana’oi matukar suka yi rijista damu suka zama membobinmu ta hanya cika ka’idojinmu da sharudanmu insha Allah.”
Daga karshe, mahalarta taron sun yi tambayoyi masu yawa da bada shawarwari, sannan an sami Sabbin membobi da suka sayi fom din zama cikin dandamalin.