Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Wakilan Kafafen yada labarai, watau (correspondents chapel) dake karkashin Kungiyar ‘yan jarida ta kasa ( NUJ) reshin Jihar zamfara ta yi kira ga bangarorin gwamnati da masu hannu da shuni da kungiyoyi masu zaman kansu da su ceci rayuwar wani jaririn dan wata tara da aka haifa babu wuri bayan gida da fitsari.

Shugaban Kungiyar a Jahar Zamfara, Kwamared Sani Haruna Dutsinma ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake mika tallafin kudi naira dubu hamsin ga iyayen jaririn a matsayin nasu taimakon domin yimasa aiki.

Sani Dutsinma ya ce, an haifi yaron ne babu wurin yin bayan gida wanda ke da wuyar fitar da abin da ya ci, hakan ya sa iyayensa suka kai shi Asibitin kwararru na Yariman Bakura inda aka turasu cibiyar kula da lafiya ta tarayya FMC Gusau domin neman magani, amma daga bisani aka mayar da shi asibitin koyarwa na Usumanu Danfodio dake sokoto.

Mahaifin yaron Malam Lawali Ibrahim ya shaida wa manema labarai cewa, an kashe Naira dubu dari uku a UDUS domin yimasa aikin gaggawa don ya samu damar yin bayan gida na wuchin gadi.

Malam. Lawal ya ci gaba da cewa bayan gwaje-gwajen lafiya da bincike da aka yi a asibitin koyarwa na Usmanu Danfodio Sokoto, da kuma kashe naira dubu dari uku ga yi wa yaron aikin gaggawa domin samar da hanyar yin bayangida wucin gadi a gefen hakarkarin sa (yaron).

A cewarsa, babu wani abin da ya rage masa face ya sayar da babur dinsa da yake amfani da shi wajen yin okada don ciyar da iyali domin hidimar yaron, ya ce ‘yan uwansu sun ba da gudunmuwar abunda suke da shi bakin karfinsu amma abun yachi tura.

Har ila yau yayi kira ga Gwamnatin Jihar Zamfara da masu hannu da shuni da Hukumar Zakka da wakafi da kungiyoyi masu zaman kansu, da kungiyar Likitoci ta kasa, da su taimaka masu domin ceto rayuwar wannan jariri.

Malam Lawali Ibrahim ya kuma yaba da kokarin kungiyar ta NUJ Correspondents Chapel na sanar da jama’a halin da lafiyar yaron ke ciki tare da bayar da tallafin kudi naira dubu hamsin a matsayin taimakonsu.

Ya yi kira ga masu son taimakawa su kira Shugaban NUJ na Jihar Zamfara Kwamared Ibrahim Musa Maizare ta 08099010064 ko Sani Haruna Dutsima ta wannan lambar 08067883434 ko Mataimakin Shugaban kungiyar Yanjaridu na kasa shiyya Arewa maso yamma, Comrade Abdulrazaq Bello Kaura a kan 070850151385 ko Kuma Ibrahim Muhammad Kanoma akan 08131996300.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *