Daga Bello Hamza, Abuja

Anbukaci dukkan rundunonin tsaron Nijeriya su hada kai don tabbatar da an gudanar da sahihin zave ba tare da tashin hankali ba, Babban Kwamandan Rundunar Samar da Zaman Lafiya da aka fi sani da ‘Nigerian Peace Corps’ Dakta Mustapha Muhammad Abubakar ya bayyana haka a tattaunawarsa da manema labarai bayan sun kammala taron shirye-shiryen na yadda za su fuskanci babban zaben da za a gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu 2023.

Ya kara da cewa, a halin yanzu babban zaben 2023 na kara fuskanto mu a kan haka ya kamata dukkan rundunonin taron kasar nan su yi aiki tare da sauran takwarorinsu da kuma dukkan masu ruwa da tsaki kamar sarakuna gargajiya, kungiyoyi masu zaman kansu, dattawa a cikin al’umma don tabbatar an gudanar da sahihin zabe ba tare da magudi ko tashin hankali ba. Ta haka ne al’umma za su karbi sakamakon zaben ba tare da tashin hankali ba”.

Dakta Mustapha Muhammad Abubakar ya kuma nemi al’umma Nijeriya su guni tashin hankali a yayin da ake gudanar da zaben da kuma lokacin da aka sanar da sakamakon zaben, ya kuma nemi al’umma taimaki jami’an tsaro da bayanai na sirri wadanda za su kai tarwatsa aniyar masu neman tayar da hankali a sassan Nijeriya.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *