Daga Nasiru Adamu
Shahararriyar makarantar nan mai suna Zirwatul Mu’ariful Wathfizul Kur’an dake Babban layi Hayin Dogo Samaru ta sake yaye dalibai 13 a karo na 3
Sheik Murtada Aliyu Jabbage daga Jihar Zamfara, shi ya zamo babban bako mai jawabi yayin da ya yi tsokaci akan muhimmancin karantar da kananan yara karatun alkur’ani
Hakanan shiehin malamin ya jawo hankaili daliban da suka sami nasarar kammala karatun kur’anin da su kasance masu maida hankali wajen bibiyar sa yau da kulum tare da ci gaba da nazartan wasu litattafan addinin musulunci don sanin yadda za su kara gyara alakarsu da mahaliccin su
Shiko shugaban kwamitin gudanarwan makarantar Farfesa Garba Ibrahim ya yi wa Allah godiyane a bisa yadda makarantar ke samun ci gaba a karkashin kulawar da suke mata tsawon shekaru batare da samun matsalaba.
Sannan daga karshe ya yi kira ga masu hannu da shuni da su ringa taimakawa makarantun addinin musulunci a duk inda suke, dun samar da nagartacciysr al’umma
Hakanan shima shugaban Malaman makarantar Barista Adamu Abdullahi, ya yi kira ga iyayen daliban makarantar da su ringa maida hankali wurin biya wa yayansu kudin makaranta, domin yin haka yana kara wa yaro hazakar gane karatun da ake yi masa. Injishi.