Daga Ibrahim Muhammad Kano

Bude bangaren hada-hadar magunguna a Sabuwar Kasuwar zamani ta Kanawa”Kanawa economic city”zai kawo tsaftace harkar magani.Dokta Abdullahi Gambo. Daraktan ayyuka na Kasuwar zamani ta Kanawa ya bayyana hakan da yake. zantawa da yan jarida bayan Gwamnan jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamarda bude kasuwar.

Yace a tsarinda suke na ginin kasuwar a karkashin kamfanin Brains&Hammers shine za’a ginawa yan bangaren kasuwar Magani kantuna 2,100,00 sunada rukunin kantuna guda Shida da za’a gina yanzu an kammala gina Biyu.

Dokta Abdullahi yace akwai kuma bangaren yan kasuwar Kantin kwari suma ana shirin za’a gina musu kantuna samada 4,000.Tsarin kasuwar zata kunshi Kantuna guda 30,000 ne.

Ya yi nuni da cewa yanzu haka duk mai son ya mallaki shagon magani a kasuwar, akwai a kasa ko na yan kantin kwari dana masu wayar hannu na GSM, akwai mutane da dama yanzu haka sun fara saya.

Yace sun hada kai da bankin Ja’iz da suke bada bashi mara ruwa,in ka bada kashi daya bisa hudu na biyan kudin kanti,su kuma zaka biya sauran a hankali ba tareda ruwa ba.

Yace dalilin gina kasuwar dan a saukakawa mutane harkar kasuwanci ne,ta samarda kyakkyawan yanayi,domin bincike ya nuna cewa kashi Takwas cikin 10 duk na wadanda suke ciniki a cikin Kano,ba daga Kano suke ba daga wajenta suke, wasu ma daga makotan kasashe suke zuwa.

Daraktan ayyukan na “Kanawa Economic City” Yace saboda haka masu shigowa na bukatar daga sun shigo ba tareda wahala ba su sami kasuwa,ita kuma kasuwar Kanawa tana kan babbar hanya ne ta bangarori daban-daban da shigowa cikinta zai sauki kenan, ba kamar yanda kasuwannin Kano suke a cunkushe yanzu ba.Sannan kuma wata dama ce ta sake fadada kasuwanci a Kano.

Ya kara da cewa, yanzu bude bangaren kasuwar na yan magani da akayi zai rage ta’ammali da kwayoyi da har ake danganta jihar Kano da cewa itace kan gaba a tu’ammali da kwayoyi a kasarnan harma ta kai ga matan aure ma suna shaye-shaye.

Ganin haka nema Gwamnatin Kano ta tsayin daka,domin taso da masu harkar magunguna ta kebesu a wannan kasuwa, dan kulawa da ganin duk magani da zai shigo.ya zama tsaftatacce ne,kazantacce ba zai shigo ba,sannan kuma zai taimakawa a kama masu kawo magunguna masu cutarwa.

Dan haka nema kasuwar keda ofisoshin jami’an NDLEA,NAFDAC,Masu kula da harhada magunguna ta kasa da zasu duba duk magungunanda za’a shigo dasu gaba daya, tun daga bakin kofa shiga kasuwar.Magani duk daga inda aka sayoshi a ciki da wajen kasarnan kasuwar zai zo ,ba zai tsaya a ko’ina ba, sai an kawo an duba a kasuwar an tabbatar mai kyaune.

Pic.
Dokta.Abdullahi Gambo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *