Daga Ibrahim Muhammad Kano

An bayyana cewa masu hada-hadar magunguna sun saba da ganin yanayi na sauye-sauye a harkokin tafida harkokinsu dan ko a baya ma shekaru samada 10 an sauya musu matsuguni.Shugaban shugunan magunguna na Zangon Kabo. Alhaji Bashir Abdurrahman ya bayyana hakan ga yan jarida.

Yace wannan mai dasu sabuwar kasuwar Kanawa yanzu shine akayi musu a cikin sauki, babu fitina a ciki, tunda dama abune na kyakkyawan tsari da akazo musu dashi da sukeda bukata.

Yace su fatansu Allah yasa dawo dasu kasuwar ya zame musu alheri a tare dasu,idan kuma wata jarabawa ce,ya basu iko da iya daukarta kuma sunada kyakkyawan fatan idan ma jarabawace da alheri ce zata zo musu.

Alhaji Bashir Zangon Kabo yace Gwamnati ta basu dama tun a shekarun baya, ta fito musu da tsarin yanda zasu mallaki wurin, ba wanda aka hana,amma duk yanda ka kai ga son ka sami wuri in bakada rabo a ciki,ko ka samu sai ya kubuta daga hannunka.

Zangon Kabo. ya yi nuni da cewa a sana’arsu ta magani su dama tamkar dangin juna suke, ana taimakawa juna dan a sami rufin asiri na rayuwa.

Alhaji Bashir yace su a mu’amalarsu ta magani abokan huldarsu na Kauye dana Birni sune a gaba dasu, su hadiman abokan cinikinsune,Shi yasa kowane lokaci suke fatan alkhairi ga abokan huldarsu.

Alhaji Bashir yace dan Zangon Kabo sunane da kowa zai iya yiwa kansa lakabi dashi,domin yau in baka da abokin hulda, za’a iya mantawa da sunan, amma inda abokin ciniki zangon Kabo zata habaka takai kowane irin wuri.

Pic.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *