Daga Bello Hamza, Abuja
A ranar Asabar 11 ga watan Fabrairu ne wata kungiya mai suna Arewar Mu Duniyar Mu ta karrama tare da nada Injiniya Hassan Mohammed Sarkin Yakin Garkuwan Keffi a matsayin Matawallen Arewa a wani kasaittaciyar biki da aka yi a fadar mai martaba Sarkin Bauchi Dakta Rilwanh Sulaiman wanda Wakilin Bauchi Alhaji Ado Garba ya wakilci Maimartaba wajen biki.
Injiniya Hassan Mohammeed wanda dan asdalin jihar Yobe ne ya samu karramarwar ne sabo yadda yake tallfawa rayuwar al’umma a duk inda ya samu kansa.
A jawabinsa bayan an kammala bikin, Injiniya Hassan ya nuna godiyarsa a kan sarautar da aka bashi na Matawallen Arewa, ya yi alkawarin ci gaba da aiki tukuru don ganin matasa sun kubuta daga dukkan abubuwan da ke bata rayuwar su, ya ce, bunkasa rayuwar al’umma shi e babban burinsa a kowanne lokaci, zai kuma ci gaba da yin haka ba tare da nuna banbanci ba. Ya kuma mika godiyarsa ga kungiyar a kan nada shi da suka yi.
A nasa jawabin, Sadaukin Garkuwan Keffi ya ce, wannan karramawar da aka yi wa Injiniya Hassan Mohammed ba abin mamaki ba ne, musamman in aka lura da yadda yake tallafa wa al’umma babu dare babu rana. Ya kuma mika godiyarsu ga Ambasada Tukur Yusufu Buratai CFR tsohon shugaban rundunar sojojin Nijeriya kuma Garkuwan Keffi tare da dimbin wadanda suka samu halartar taron, kamar su Bulama Ibrahim Buratai, Sultan Alhassan, Col. Haruna Idris Zaria, Ibrahim Sani Garba, da kuma Injiniya Usman Ahmed Injiniya Hassan Geidam, Injjiniya Adamu Bahago Dagona, Zanna Dapchi, shugaban karamar hukumar Bursari, da dan majalisa wakilai, Hon Kabir Lawal Jarman Garkuwan Keffi, Engr Mohammed Abbagana, Engr Hassan Bilal, Surv. Ali badema, Surv. Hassan Gambo, Ali Alh Audu P.A, Musa Jajere, Engr adamu Idi, Engr Idriss Yerima, Engr Adamu ibrahim, Engr Mohd Ibn Adam, Mohammed Hassan Jajere.
An buga kwallon kafa tsakanin TY Buratai Football Academy da Wikki Tourist Bauchi a filin was ana Tafawa Balewa Bauchi don karramar sabon matawallen Arewa, inda TY Buratai Football Academy ta blallasa Wikki Tourist da ci 4 babu ko daya. An kuma yi rayerayen gargaji danam daban.