Daga Ibrahim Muhammad Kano.

Iyayen dalibai dake makarantun sakandiren yan mata sake jihar Kano na kukan cewa wasu shugabannin makarantun na tilastawa dalibai biyan wasu kudade a daidai lokacinda Gwamnatin jihar Kano ke kwakwazon cewa ta gudanarda tsarin ilimi kyauta kuma dole.

 

Sun koka da cewa wani abin tada hankalin shine yanda a wasu makarantun ake hana dalibai su shiga aji su zana jarabawar gwaji domin kawai an samu tsaiko iyayensu basu biya kudinda makarantun suka kallafa musu sai biya ba da suna kudin PTA.

 

Binciken jaridar idon mikiya ta gano cewa wasu shugabannin makarantun sun fake da karbar irin wadannan kudade suna kawo nakasu ga ilimin dalibanda iyayensu suka kasa biya a daidai lokacinda makarantar keso a biya sai a korasu gida.

 

Wani Uba da irin wannan ta shafa a makarantar sakandiren yan Mata ta Kuka Bulukiya da fafur shugabar makarantar ta hana diyarsa zama tayi jarabawar ta korata gida.

 

yace abin takaicin shine yanda yaje neman a daga masa kafa a bar yar tasa shiga aji in yaso inya sami faraga sai yazo ya biya kamar yanda yake a baya, amma shugabar makarantar taki dole ya dawo da yar gida.

 

Sai dai wasu na ganin tamkar wasu shugabannin makarantun ne ke yiwa shirin Gwamnati na ilimi kyauta kuma dole zagon kasa ko kuma Gwamnatince me furta bada ilimin kyauta a baka ba,a aikace ba.

 

Mun nemi ji daga kwamishinan ilimi na jihar Kano.Ya’u Yanshana da shugaban hukumar kulada makarantun sakandire Dokta Bello amma har zuwa rubuta labarin bamu sami ji daga garesu ba.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *