Daga Ibrahim Muhammad Kano.

Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta kama bindigu kirar AK-47 guda 4 a wani samame da suka kai a Kwanar Garko da ke karamar hukumar Garko a jihar Kano a kan hanyar Kano zuwa Bauchi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a aka rabawa yan jarida.

Sanarwar ta ce, an kwato bindigogin ne a lokacin da rundunar ta kama wani direban motar safa da ke kokarin sauya alkibla yayin da daya daga cikin fasinjojin ya sauko rike da wani abin tuhuma.

Bayan da tawagar ta mayar da martani cikin gaggawa, wanda ke cikin motar ya jefar da kayan, ya tsere daga wurin.Da aka gudanar da bincike, an gano buhu dauke da bindigogin AK-47 guda hudu,” inji shi.

Rundunar ta ce za ta kara kaimi wajen kamo wanda ya gudun, ta kuma bukaci mazauna yankin da su ci gaba da kai rahoton duk motsi ko kayayyaki da ba su yarda da su ba, zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa.

Sannan kuma rundunan yan sandan za’a iya yi musu .na gaggawa da ga cikin wadannan lambobin na gaggawa, 08032419754, 08123821575, 0807609127 da 09029292926

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *