Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Kwamandar hukumar yaki da yan ta,adda Bello Bakyasuwa, ya tsallake rijiya da baya a kan hanyarsa daga Gusau zuwa Kaduna, a lokaci da wasu da ba’a san ko su waye ba suka tare shi a Kan hanya a lokacin da zai bar gari.

Hakan yana kunshe ne cikin wata takarda Mai dauke da sa hannunsa wadda ya rabata ga manema labarai a garin Gusau, ya Kara da cewa, a halin yanzu yana kwance a gadon asibiti, ya ce rayuwanshi na cikin hadari, in da ya Kara da cewa yana fuskantar barazana a koda wani lokaci.

Bakyasuwa, yace yadda abin ya faru shine, kwanaki hudu da suka wuce a kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Funtua-Zaria, sai ya lura cewa motoci biyu kirar Hilux da BMW suna bina shi a baya, sai ya tsaya a Yankara suka wuce shi.

Ya ce  “Mutanen da ke cikin motocin biyu ne suka fara harbin motar da nake ciki, bayan na ci gaba da tafiya kuma na samesu a hanya, mun kwashe ‘yan mintuna muna musayar wuta da su sai da na tsere na gudu cikin daji duk jikina jini.”

Saidai daga bisani bayan kamar mintuna 15, ‘yan sanda suka zo wurin da abin ya faru suka kubutar da ni aka kai ni wata cibiyar lafiya a wani kauye da ke kusa.

Bakyasuwa, ya bayyana cewa yana zargin wasu ‘yan siyasa ne ke daukar nauyin maharan, saboda a cewarsa a watannin baya wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan direbansa a Gusau kan hanyarsa daga Command Guest-Inn zuwa Anguwar Gwaza suna tafiya da motar ofishinsa.

Daga karshe yayi  kira ga hukumomin tsaro da su kawo masa agaji, domin rayuwasa na cikin hadari Kuma ya bukacesu dasu gudanar da kwakkwaran bincike don kama wadanda suka kai masa harin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *